✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen miji sun hau jirgi daga Indiya zuwa Amurka don dukan surukarsu

’Yan sandan florida ta kasar Amurka sun ce sun ceci wata mata ranar asabar din  da ta gabata, wadda mijinta da iyayensa suka hawo jirgi…

’Yan sandan florida ta kasar Amurka sun ce sun ceci wata mata ranar asabar din  da ta gabata, wadda mijinta da iyayensa suka hawo jirgi tun daga Indiya don su yi mata duka.

Shugaban ’yan sanda na Hillsborough, ya ce Siky Gaind mai shekara 33 ta kira iyayenta a waya a can Indiya inda ta bayyana musu cin zarafin da aka yi mata. Daga suka kira mahukunta suka sanar da su. 

’Yan sanda sun ce mijin matar Decbir Kalsi mai shekara 33 da iyayensa Jasbir mai shekara 67 da Bhupinder Kalsi mai shekara 61 sun yi garkuwa da Gaind a gidansu da ke Ricerciew. Iyayen mijin sun ce sun yi takakkiya ne daga Indiya don taimaka wa dansu “ya ladaftar da matarsa saboda rashin biyayyarta.”

Da mataimakin shugaban ’yan sandan ya isa gidan babu wanda ya bude kofa. Da Gaind ta yi yunkurin bude kofar, ta kuma yi ihu don a taimake ta tare da ’yarta ’yar shekjara guda, sai kawai ya kutsa kai cikin gidan duk da cewa Kalsi na ta kokarin kulle kofar. Lokacin da jami’in ’yan sanda ya yi kokarin daura wa mijin matar ankwa sai iyayensa suka tunkare shi, kamar yadda kafar labarai ta Tampa Bay Times ta ruwaito.

Kalsi da Gaind tai sun yi ta takaddama inda ya yi mata dukan tsiya a Juma’ar makon jiya, sannan iyayensa suka yi mata barazana. Har takai ga an mangari jaririyarta lokacin da take rike da ita.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa akwai yiwuwar Decbir da Jasbir Kalsi za su fuskanci tuhumar tsare mutum da keta haddin yara, sannan suka karyata neman taimakon da aka bijiro wa lambar 911,” kamar yadda aka ruwaito daga Tampa Bay Times.