✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Izala ta musanta hana Dahiru Bauchi yin Tafsir a Kaduna

Shugaban Kungiyar Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah ( JIBWIS) a jihar Kaduna Shaikh Muhammad Tukur Isa ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada…

Shugaban Kungiyar Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah ( JIBWIS) a jihar Kaduna Shaikh Muhammad Tukur Isa ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa, Gwamnar Jihar Nasir El-Rufai zai hana Shaikh Dahiru Bauchi yin tafsir a jihar.Ya ce, masu yaxa irin wannan labari makiya zaman lafiya ne masu neman tada husuma dan saboda siyasa.

Shaikh Tukur Isa ya kuma bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a jihar Kaduna.

Ya ce, wannan zance babu kanshin gaskiya  domin kuwa babu inda kungiyar Gamayyar  Sunnah da suka taba zama da Gwamnan Jihar domin tattauna wannan batu na hana Shaikh Dahiru Bauci zuwa tafsir Kaduna.‎

Aminiya ta samu labarin cewa akwai wata sanarwa da ke  yawo a shafukan sada zumunta dake nuna wai Gamayyar Malaman sunna sun zauna da Gwamna El-rufai suka gindaya masa sharudda cewa sai an hana Shaikh Dahiru Bauchi yin tafsir a Kaduna kafin su goya masa baya a sake zabarsa.