✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jajantawa ga wadanda ambaliya ta shafa

Assalamu alaikum Edita, da fatan kuna cikin koshin lafiya ina son ku ba ni dama in jajanta wa ’yan uwanmu talakawan Najeriya. Hakika wannan lamari…

Assalamu alaikum Edita, da fatan kuna cikin koshin lafiya ina son ku ba ni dama in jajanta wa ’yan uwanmu talakawan Najeriya. Hakika wannan lamari na ambaliyar ruwa da ta yi asarar rayuka da dukiyoyi da muhallan al’umma abin juyayi ne. Muna fata Allah Ya mai da mafificin alherinSa ga ’yan uwanmu da suka yi hasarar dukiyoyi da muhallansu. Kuma Allah Ya gafarta wa wadanda suka riga mu gidan gaskiya, amin. Da fatan gwamnatin Najeriya za ta yi wani abu na ba da tallafi ga wadanda wannan bala’i ya shafa. 

Daga Arabiyyu Muhammad Gidan Madi, Jihar Sakkwato. 08067873852/09032385555.