✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Jaki mai wayo’

Assalamu alaikum Manyan Gobe, yaya hutu? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “Jaki mai wayo.” Labarin yana nuni…

Assalamu alaikum Manyan Gobe, yaya hutu? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “Jaki mai wayo.” Labarin yana nuni ne kan yadda  mai wayo da dabara ke samun mafita a duk lokacin da ya shiga matsala. A sha karatu lafiya.

Taku: Amina Abdullahi.

An yi wani manomi wanda ke  da tarin dabbobi a gonarsa. A cikin dabbobin nasa akwai wani tsohon jaki wanda a kullum yake janyo masa matsala.

Jakin ya kasance ba ya iya jure wahala musamman wajen daukar kayan aikin gona masu nauyi. Hakan ya sanya manomin ya ji jakin ya fitar masa a rai.

Ran nan kamar kullum manomi ya fito gonarsa tare da sauran dabbobi, yana cikin nuna musu hanyar da za su bi  sai wannan tsohon jaki ya fada a cikin rijiya.

Wannan abu ya bata wa manomin rai matuka inda ya yanke shawarar  barin jakin a cikin rijiyar. Sai ya nemi mutane su taimaka masa da zuba datti domin a cike rijiyar.  Abin mamaki shi ne duk da an cike rijiyar da bola sai aka ga jakin ya fito yana kakkabe jikinsa.

Hakan ya ba mai jakin da kowa mamaki, inda aka tabbatar jakin ya nuna wayo da fasaha a lokacin da ya ga mutuwa.

Da fatan Manyan gobe za su kasance masu dabara da wayo a duk lokacin da suka tsinci kansu wajen fuskantar kalubalen rayuwa.