✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jakuna: Abin hawa a Arewa, nama a Kudu

Duk wanda ya ce kasar nan za ta tarwatse, yana shirme ne kawai, domin mutanen kowane yanki suna dorago ne da sauran yankunan don biyan…

Duk wanda ya ce kasar nan za ta tarwatse, yana shirme ne kawai, domin mutanen kowane yanki suna dorago ne da sauran yankunan don biyan bukatunsu na yau da kullum tun shekaru aru-aru.
Misali Arewa tana kunshe da manoma da makiyaya da yalwar kasar noma da kasuwancin dabbobi da sauran ababuwan bukatun jama’a baya ga yawan jama’a.
Can kuma Kudu musamman Gabashin kasar nan na da kayan lambu da manja, sannan mutanensa sun kware a harkar kasuwanci a duk lungunan kasar nan.
Yankin Yarbawa kuwa wato Yamma na da teku da ke taimakawa wajen hada-hadar kasuwanci kuma yankin ya yi fice a harkar ilimin zamani saboda doguwar alakarsu da Turawa.
 Idan ka zauna za ka ci sakwara, doyar na iya zamowa an noma ta ce ko a Binuwai ko Lafiya ko kasar Zazzau da sauransu. An samun kanwa daga Borno da Yobe, manja daga Inugu, kayan miya daga Kano ko Sakkwato, kayan yaji daga Kaduna da Katsina, kifi daga Maiduguri da Adamawa, agushi daga Kogi da Kwara, kananzir daga yankin Neja-Delta.   
Wadannan kayayyakin abinci ana fataucinsu tun shekaru aru-aru, tun ana tafiya a kasa har aka zo kan dabbobi da motoci da jiragen kasa.
Malam Bahaushe yana amfani da jaki a matsayin dabbar dakon kaya daga gona ko wani bangare zuwa wani bangaren tun kafin zuwan mota, kuma har yanzu a hanyar da mota ba ta iya bi, a yankunan karkara haka lamarin yake.
Sai dai abin mamaki shi ne yadda ake safarar jakuna a cikin manyan motoci a tsaye ko kwance an daure musu kafafuwa don kai su inda za su zama nama, shi ne abin da ya bambanta Arewa da Kudu.
 A kwanakin baya irin wannan mota ta shigo shataletalen da ke kan titin Legas a tsakiyar birnin Kaduna inda ta yi kwanciyar magirbi ta zubar ta wasu, ta raunata wasu, ta halaka wasu sannan wasu kuma ko kwarzane ba su yi ba.
Hadarin ya afuku ne da daddare, inda motar mai lambar Legas, dk 418 AKD ta jawo aka rufe hanyar da ta nufi gadar Kaduna.