✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an Imigireshen 61 sun samu karin girma a Jihar Katsina

A ranar Talatar da ta wuce ne  jami’an Hukumar Kula da Shigi da Fici (Imagireshin) 61suka samu karin girma a mukamai daban-daban a Jihar Katsina.…

A ranar Talatar da ta wuce ne  jami’an Hukumar Kula da Shigi da Fici (Imagireshin) 61suka samu karin girma a mukamai daban-daban a Jihar Katsina.

Kamar yadda Kwanturolan Hukumar Joshua Olusola Ajisafe ya ce, wannan karin girma da jami’an suka samu ya biyo bayan kwazon da suke nunawa ne wajen gudanar da ayyukansu.

Ya kara da cewa karin girma wani abu ne da yake fitowa daga Allah, su ma wadanda ba su samu ba su yi hakuri lokacinsu na zuwa.

Mista Joshua ya ce, hujkumar tana godiya ga  Babban Kwanturola na Kasa Muhammad Babandede bisa yarda da amincewar da ya yi a kan ciyar da wadannan ma’aikata gaba.

Da ya juya a kan wadanda suka samu karin girman har da wadanda ke jiran nasu da wadanda ake cikin tantancewa, ya ja hankalinsu cewa su zage damtse wajen aiwatar da aikinsu kamar yadda suka yi alkawari.

Ya ce jami’ansa za su ci gaba da sanya ido a kan iyakokin da ke jihar domin tabbatar da karin tsaro da kuma hana shiga ko fita ba bisa ka’ida ba.

Ya yi kira ga jama’a su rika bai wa jami’an rahoton duk wani mutum ko gungun mutanen da ba su amince masu ba da sunan cewa baki ne.

Da yake jawabi a madadin sauran wadanda aka yi wa karin girman, Mataimakin Kwanturola wanda ya zama Na’ibin Kwanturola Ahmed Umar Kibiya ya  gode wa Allah da Ya kai su ga wannan matsayi. Sannan ya gode wa hukumarsu tun daga kasa har sama a kan irin hadin kai da taimakon da take ba su wanda ya sa har suka samu wannan karin girma.

Ya ja hankalin wadanda ba su samu ba a yanzu kan su ci gaba da yin hakuri da nuna jajircewa har zuwa lokacin da nasu zai fito.

Sannan ya ce za su ci gaba da nuna kwazo a wajen gudanar da aikinsu kamar yadda suka saba musamman a game da wadanda suke shigowa ko zama cikin kasar nan ba bisa ka’ida ba.

Wadanan jami’an da aka kara wa girma sun taka muhimmiyar rawa wajen hana masu shiga da fita bisa ka’ida ba musamman a kan hanyar Kwangwalam zuwa Maimujiya, musamman masu safarar mutane da  namiyagun kwayoyi a wannan hanya da ta yi iyaka da Nijar.

Sauran wadanda aka yi wa karin girmar sun hada da Kakakin Hukumar Kasim Ilyasu da Nalami Magaji wadanda suka tashi daga manyan Na’iban Sufurtanda zuwa Sufurtanda, sai Goma Bala da ya zama Babban Sufurtanda. Bashir Abdullahi da Suleiman Ishak na daga cikin mutum 61 da suka samu wannan karin girma.