✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Akwa Ibom ta kori malamai 8 kan badala

Hukumar Jami’ar jihar Akwa Ibom, ta tabbatar da hukuncin kora a kan malamai 8 bisa zargin laifukan da suka hada da neman mata dalibai. Shugaban…

Hukumar Jami’ar jihar Akwa Ibom, ta tabbatar da hukuncin kora a kan malamai 8 bisa zargin laifukan da suka hada da neman mata dalibai.

Shugaban Jami’ar Farfesa Eno Ibanga ne ya sanar da hakan a jami’ar a Ikot Akpaden da ke karamar Hukumar Mkpat Enin jihar Akwa Ibom, inda ya ce an kori malaman jami’ar ne saboda neman mara daliban jami’ar da suke yi.

Farfesa Eno, ya kara da cewa a yazu haka an kai karar wasu dalibai 10 da aka kama da hannu wajen yin asiri jami’ar.

An dai kama daliban da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne dauke da wata karamar makara da jan kyalle da kuma gatari, lokacin da suke kokarin shirya wani biki.