✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Gombe ta ɗaga likafar malamai huɗu zuwa matsayin Farfesa 

Ana duba yiwuwar ɗaga likafar wasu manyan ma’aikatan jami’ar 41 zuwa matsayi na gaba.

Jami’ar Jihar Gombe (GSU) ta ɗaga likafar malamai huɗu zuwa matsayin Farfesa yayin da 18 suka zama mataimakan Farfesa wato Readers.

Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar wanda kuma shi ne Uban Jami’ar, Sanata Joshu’a M Lidani ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da jami’ar ta kira.

Ya ce Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya bai wa jami’ar cikakken ’yancin gudanar da harkokinta ba tare da ya sa ma ta baki ba.

Lidani ya ce bayan malamai 22 da aka ƙarawa girma, majalisar gudanarwar ta kuma ƙara wa wasu ma’aikata 85 girma a matakai daban-daban

A cewar Lidani, ƙarin girman ya fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Oktoba shekarar 2023.

Kazalika, majalisar ta ba da dama a duba yiwuwar ɗaga likafar wasu manyan ma’aikatan jami’ar 41 zuwa matsayi na gaba.

Ya ƙara da cewa, akwai ma’aikata waɗanda ba malamai ba guda 57 da su ma aka amince a ɗaga likafar su.

Sanata Joshua Lidani ya kuma jinjina wa Gwamna Inuwa Yahaya kan yadda ya magance matsalar zaizayar ƙwarin da ya addabi jami’ar.

Ya kara da cewa gwamnan ya amince a samar da sashin kimiyyar muhalli a reshen jami’ar da aka gina a garin Dukku.