✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Jami’ar Jihar Gombe ta bunkasa cikin kankanen lokaci’

Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jihar Gombe Farfesa Idris Muhammad dan Isan Gombe ya ce jami’ar ta samu ci gaba cikin kankanen lokaci da kafa ta.Farfesa…

Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jihar Gombe Farfesa Idris Muhammad dan Isan Gombe ya ce jami’ar ta samu ci gaba cikin kankanen lokaci da kafa ta.
Farfesa Idris Muhammad, ya bayyana haka ne a Gombe, bayan kwamitin ya kammala zamansa na wata hurhudu a dakin taro na hukumar.
Ya ce a shekara biyar da suka gabata jami’ar ta samu wannan ci gaba sosai a bangaren gine-gine masu inganci kamar a Amurka. “Wadannan gine-gine na dakunan kwanan dalibai, benaye masu hawa uku-uku an yi su ne bayan nada su jagorancin jami’ar shekara biyu da rabi da suka gabata, kuma kowane rukunin daki zai dauki dalibai 1,600 mutum hudu a daki daya,” inji shi.
Sai ya gargadi daliban jami’ar su guji sayar wa wasu daliban wuraren kwanansu wato don gudun lalata dakunan kwanan.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Ibrahim Musa Umar ya ce jami’ar na fama da matsalar kudi amma an samu ci gaba sosai ta yadda jami’ar take iya bugun kirji da kowace jami’a a kasar nan wajen samar da ingantaccen ilimi.