Search
Subscribe
Jami’ar Muhammadu Buhari mai zaman kanta

Jami’ar Muhammadu Buhari mai zaman kanta

A ranar Asabar da ta gabata ce Uwargidan Shugaban Kasa A’isha Muhammadu Buhari ta bayyana niyyarta ta bude jami’a mai zaman kanta da za ta sanya wa suna ‘Jami’ar Muhammadu Buhari.’

Hajiya A’isha Buhari ta bayyana wannan niyya tata ce a yayin wani taro na masu ruwa-da-tsaki da aka yi a garin Yola na Jihar Adamawa a ranar Asabar din.

Sai dai kuma Uwargidan Shugaban Kasar ba ta fadi lokaci da wurin da za a bude jami’ar ba, sai dai ta ce za ta bude jami’ar ne da hadin gwiwar kasashen Sudan da Katar.

Abin da ya jawo hankalin jama’a game da wannan yunkuri na Uwargidan Shugaban Kasa shi ne yadda ta himmatu wajen ganin an bude jami’a mai zaman kanta maimakon ta taimaka wajen ganin an gyara jami’o’in gwamnati da ake da su a fadin kasar nan wadanda a halin yanzu suke cikin mawuyacin hali.

A duk lokacin da kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta umarci ’ya’yanta su shiga yajin aiki, babban dalilin da take bayarwa shi ne babu kayan aiki na zamani da sauran muhimman abubuwan koyarwa da kuma bincike a jami’o’in kasar nan. Da kamata ya yi Uwargidan Shugaban Kasa ta tashi tsaye wajen ganin an inganta jami’o’in da ake da su mallakar gwamnati wadanda ’ya’yan talakawa za su iya amfana da su, maimakon kafa jami’a mai zaman kanta wadda sai ’ya’yan wane da wane za su iya zuwa su yi karatu a cikinta.

A lokacin yakin neman zabe Jam’iyyar APC wadda Shugaba Buhari ya ci zabe a karkashinta ta rika yi wa dan takarar Shugabancin Kasar a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar shagube cewa ya bude jami’a nai zaman kanta a Yola Jihar Adamawa wadda ta fi karfin dan talaka,  maimakon ya yi amfani da damar da ya samu  na kasancewarsa Mataimakin Shugaban Kasa na tsawon shekara takwas domin ganin an inganta jami’o’i mallakar gwamnati, amma bai yi haka ba, sai ya kafa tasa ta kansa yana samun kudi da ita.

Kwatsam kuma sai Uwargidan Shugaba Buhari ita ma ta fito ta nuna tana so ta yi koyi da shi Atiku wanda jam’iyyar maigidanta take ganin bai yi daidai ba da ya bude jami’a mai zaman kanta mallakarsa.

Takawan Najeriya sun nuna wa Shugaba Buhari cikakkiyar soyayya ce saboda suna ganin shi ne kawai zai ceto su daga mawuyacin halin da suke ciki, amma sai ga shi daga cikin gidansa ana neman kwance musu zane a kasuwa.

Sanin kowa ne cewa jami’o’i masu zaman kansu kudi suke nema, domin sai da kudin ne za su iya biyan albashin malamai da sauran ma’aikatan jami’ar da kuma gudanar da harkokin yau da kullum na jami’ar, shi ya sanya dole su zabga kudi domin su samu damar gudanar da harkokin jami’ar har kuma su samu riba. Saboda haka ne a duk irin wadannan jami’o’i masu zaman kansu zai yi wahala a samu ’ya’yan talakawa a cikinsu, saboda al’amari ne na kudi, kudi kuma ba kadan ba.

Ba mu san abin da ya sanya gwamnati take kokarin dabbaka jami’o’i masu zaman kansu ba a daidai wannan lokaci da jami’o’in gwamnati ke bukatar kulawa ta musamman, domin ko a makon jiya Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa ( NUC), Farfesa Abubakar Abdurrasheed ya bayyana cewa, akwai takardun masu bukatar rajistar jami’o’i guda 303 a gaban hukumarsa, inda ya nuna cewa idan da zai samu dama zai yi wa dukkansu rajista. Wato dai zai kasance a Najeriya akwai jami’o’i masu zaman kansu fiye da dari hudu ke nan.

Ya kamata gwamnati ta rika lura da yadda makarantu masu zaman kansu suke gudanar da ayyukansu, domin ana bude makarantun ne domin samun riba, saboda haka duk yadda masu makarantun za su yi domin jawo hankalin iyaye su kai ’ya’yansu wadannan makarantu za su yi.

A yanzu haka daliban makarantun gwamnati da dama sun fi  so su rubuta jarrabawarsu ta fita daga sakandare (WAEC ko NECO) a makarantu masu zaman kansu domin an fi cin jarrabawar a irin wadancan makarantu, saboda hukumomin makarantun sun san irin shiga da fitar da suke yi don ganin daliban da suka rubuta jarrabawarsu a makarantun sun haye.

Wannan ne ya sanya darajar ilimi ta yi kasa a Najeriya a halin yanzu, domin  za ka ga dalibi ya samu kyakkyawan sakamako a jarrabawa amma idan aka tsare shi ya yi bayanin wasu abubuwa da aka ce ya ci sai ya kasa, idan kuma aiki ne aka dauke shi sai ya kasa, daga karshe dai dole a kore shi.

Mafi saukin hanyar da za a bi domin a kashe kasa ita ce a kashe hanyar samun ilimi ga al’ummarta, domin duk al’ummar da ta rasa ilimi ta zama koma-baya, daga karshe ma za a nemi wannan al’ummar a rasa.

Saboda haka wajibi ne gwamnati ta tabbatar ta saukaka hanyoyin samun ilimi ga jama’a, maimakon a bar shi sai mai kudi kawai zai iya samar wa ’ya’yansa ilimi mai inganci. Matukar aka bar ’ya’yan talakawa suna gararamba a titi babu ilimi mai inganci wallahi ba za su bar ’ya’yan masu hannu da shuni da suka yi karatu su zauna lafiya ba. Saboda haka ba dabara ba ce a ware ’ya’yan wadansu a ba su ilimi mai inganci amma a bar ’ya’yan wadansu suna kallo saboda iyayensu ba su da kudi ba.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin