Jami’ar Nnamdi Azikiwe, a jihar Anambra ta kori wani babban malamin jami’ar mai suna Dakta Peter Ekemezie, daga bakin aiki wanda yake sashen Kimiyyar Gwaje-gwaje da kuma na Masana’antu a jami’ar.
Mista Ekemezie, mai shekaru 46, an dauke shi aiki a jami’ar tun a matsayin malami mai daraja ta daya a watan Yulin shekarar 2010. Hukumar gudanarwar jami’ar ce ta sallame shi daga aiki, bisa abin da ta kira tafka mugun laifi da ya yi na yin bogin takaddar kammala karatun digiri na farko.
An dai yi zargin tsohon malamin ya yi amfani da takaddar jabu, wadda ya ke ikirarin ya yi karatu ne a jam’ar Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.