Da Dumi Dumi

Jami’in DSS ya kwaci kansa da kyar daga barayi

Wani jami’in tsaro na farin kaya (DSS) ya samu nasarar kubuta daga hannun masu sata a mota da aka fi sani da ’yan “One Chance,” bayan ya shiga motarsu a Abuja.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da ta gabata da misalin karfe 8 na dare kamar yadda wani da ya san mutumin kuma yake cikin wadanda suka kai masa dauki lokacin da yake gwagwarmayar kubuta, ya shaida wa Aminiya.

Ya ce barayin sun dauki jami’in ne a daura da mashigar garin Kubwa da ake kira NNPC, inda ya tsaya don shiga motar haya zuwa garin Nyanya, kuma shi ne mutum na hudu a motar ba tare da sanin ragowar ukun barayi ne ba.

“Da farko sun yi tafiya har zuwa yankin Gwarinpa a kan tagwayen hanyar Abuja zuwa Zuba, amma sai suka juyo bayan hawa gadar sama, suka sake dawowa Kubwa, inda suka tsaya a daura da wata na’urar ATM a wani banki a yankin Unguwar Gidajen Gwamnatin Tarayya da ke garin.

“Mutum biyu sun zauna tare da shi a cikin motar, yayin da na ukun ya fita da katinsa na ATM don fitar da kudi. Sai dai tafiyarsa ke da wuya sai jami’in na Hukumar DSS ya gane wajen, sai ya yunkura ya shuri gilashin daya daga cikin kofofin motar, kasancewar hannuwansa biyu na daure, kuma hakan ne ya ankarar da masu wucewa suka kawo masa dauki,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Ya ce sai dai barayin sun samu nasarar tserewa nan take, a yayin da shi kuma mutumin wanda suka yi masa raunuka uku a kai baya ga cakarsa masa wuka a hannu daya da kuma kafa gud.  An kai shi babban asibitinKubwa, aka yi masa jinyar gaggawa kafin a wuce da shi zuwa wani asibiti a daren, kamar yadda ya bayyana.

Da aka tuntubi Babban Jami’in ’Yan sandan Kubwa, CSP Ayobami Surajudeen ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an gabatar wa ofishinsu da karafunan lambar motar, wadanda aka cire daga motar gabanin jama’a su banka mata wuta. Haka wata majiya ta ce an kuma samu wayar mutumin tare da wata wayar daban a cikin motar.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya