✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar APC ta kara lashe zaben kananan hukumomi 3 a Nasarawa

Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta lashe zaben kananan hukumomi uku da suka rage a jihar. Shugaban hukumar zaben jihar Alhaji Abdullahi Sallau Moddibo ne…

Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta lashe zaben kananan hukumomi uku da suka rage a jihar. Shugaban hukumar zaben jihar Alhaji Abdullahi Sallau Moddibo ne ya sanar da haka a Lafiya a ranar Litinin da ta gabata. Ya ce adadin da jami’an gudanar da zabe suka gabatar masa ya nuna Jam’iyyar APC ne ta lashe zaben da na kansuloli a kananan hukumomi uku da ba a yi zabe ba a kwanakin baya. A yanzu Jam’iyyar APC ta samu nasara a kananan hukumomi 9 a yayin da Jam’iyyar PDP take da kananan hukumomi 4.  Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne aka gudanar da zaben kananan hukumomin jihar inda ba a samu kammala zaben a kananan hukumomin Akwanga da Nasarawa da Obi ba.