✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar APC za ta kawar da shugabanci marar kyau – Gwamna Wamakko

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce an kafa Jam’iyyar APC ne don kawar da shugabanci marar kyau a kasar nan. Gwamnan ya…

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce an kafa Jam’iyyar APC ne don kawar da shugabanci marar kyau a kasar nan. Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin taron shugabannin riko na jam’iyyar a jihar a masaukin baki na daya da ke Sakkwato.
Ya ce in aka zabi jam’iyyar ta hau mulki za ta tabbatar da sahihiya kuma ingantacciyar dimokuradiyya a kasar nan. Ya ce jam’iyyar za ta kwatanta gaskiya da adalci da bin dokoki, ba kamar yadda Jam’iyyar PDP ke yi musu karan-tsaye ba.
Wamakko ya zargi Jam’iyyar PDP da haddasa matsalolin da ke kawo rashin zaman lafiya a jihohin da ba ita ke mulki a cikinsu ba. Kuma ya bukaci masu ruwa da tsaki a jam’iyyar a jihar kan kada su yarda lagonsu ya yi sanyi kan wannan yunkuri. “Kada ku ji tsoro ko kadan, ku yi aiki tukuru don samun nasara,” inji shi. Kuma  ya ba su tabbacin samun nasara saboda yadda talakawan kasar nan ke bukatar samun canji.
Tun farko Shugaban Riko na Jam’iyyar Alhaji Inuwa Abdulkadir ya ce an kira taron ne domin duba irin nasarorin da aka samu da kara nemo hanyoyin da za a bi domin kara ci gaba.
Alhaji Inuwa ya ce mutum dubu 300 da 800 aka yi wa rajistar zama dan jam’iyyar, inda mutum 900 ke jiran rijista a cikin kudurinsu na yi wa mutum miliyan biyu rajistar zama dan jam’iyya a jihar.
Taron ya samu halartar Shugaban Majalisar Dokoki na Jihar Alhaji Lawali Zayyana da ’yan Majalisar Tarayya tara da kwamishinoni da masu ba Gwamna shawara da sauran jami’an gwamnatin jihar.