✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar PDP a Kuros Riba ta ware wa mata mukamai

A kokarin daidaita tsarin raba-daidai a jam’iyyar PDP a Jihar Kuros Riba, jam’iyyar ta ware wa mata mukamin mataimakin shugaban karamar hukuma.Shugaban jam’iyyar na jiha,…

A kokarin daidaita tsarin raba-daidai a jam’iyyar PDP a Jihar Kuros Riba, jam’iyyar ta ware wa mata mukamin mataimakin shugaban karamar hukuma.
Shugaban jam’iyyar na jiha, Ntufan John Okon ne ya bayyana haka sa’ilin da ya gana da manema labarai, inda kuma ya ce an yanke shawarar hakan ne tun da aka rantsar da shi sabon shugaban jam’iyyar. Ya yi alkawarin sai an dama da mata a kowane matakin mukami.
Ya ce, “Yanzu an ware gurbin mukamin mataimakin shugaban karamar hukuma har goma sha biyar, yayin da gurbin kamsila kuma aka ware wa mata gurbi hamsin da takwas a duk fadin jihar. Haka nan an ware musu mukamin kujerar shugaban karamar hukuma guda hudu”. Inji shi.
Ya ce yin hakan ya biyo bayan magance yawan korafin da mata kan yi ne na sai idan zabe ya zo ake tunawa da su kuma idan an ci, sai a bar su da kuturun bawa.
Ya ce a lokacinsa ba a bari kowane shugaban karamar hukuma ya yi tazarce ba, kuma babu wanda zai yi, saboda tsarin karba-karba da ake bi a jihar, lamarin da ya nuna wanda zai fito takarar mukamin gwamnan jihar bayan wa’adin mai ci yanzu, zai fito ne daga arewacin jihar, ba kamar yadda wasu ke baza jita-jita ba.
Ntufan Okon ya bayyana cewa ya je kasashen Kenya da Ruwanda da kuma Afirka ta Kudu, inda ya ga majalisun dokokinsu kashi sattin cikin dari mata ne. A kasar Kenya ma mace ce shugabar majalisar dokoki, saboda haka ya yi fatar wannan karo za a samu cikakken daidato a tsarin siyasar jihar.