✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar PDP ba zata sake yin tasiri a Kaduna ba- El-Rufai

Gwamnar jihar Kaduna Nasir Ahmed  El-Rufai ‎ ya bayyana cewa, jam’iyyar PDP ba zata sake yin tasiri a jihar Kaduna ba. A cewar Gwamnan jam’iyyar…

Gwamnar jihar Kaduna Nasir Ahmed  El-Rufai ‎ ya bayyana cewa, jam’iyyar PDP ba zata sake yin tasiri a jihar Kaduna ba.

A cewar Gwamnan jam’iyyar a shekaru 16 da ta yi babu abin da zasu nuna a jihar in ba titin Kawo mai doro daya ba.

Gwamnar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakwancin wasu ‘yan jam’iyyar da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar tabbatar masa da kujerarsa da Kotun zabe ta yi.

Ya kuma kara da cewa, Kotun ta nuna cewa su masu gaskiya sune ke da gaskiya a yayin da kuma masu karya aka tabbatar masu da cewa su makaryata ne.

“In Allah ya yarda PDP ba zata sake yin tasiri a jihar Kaduna bamu san cika yin magana domin idan Allah ya baka shugabanci abin da ya kamata kayi shi ne mayar da hankali wajen yi wa mutane aiki.” In ji shi.

‎Ya kuma ce, baya cika san yin magana akan batun almundahana da kudi da suka yi a lokacin mulkinsu.