✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyu za su kai 200 a zaben 2023 – INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ce, za a iya samun jam’iyyun siyasa sama da 200 a babban zaben shekarar 2023 a…

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ce, za a iya samun jam’iyyun siyasa sama da 200 a babban zaben shekarar 2023 a cikin takardar kada kuri’a.

Kwamishinan INEC na kasa Festus Okoye, ne ya sanar da hakan a Abuja, a wani taron bita da aka yi da kungiyoyin farar hula da Gidauniyar Kofi Annan Foundation da aka yi a Abuja.

Festus, wanda ya wakilci shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubum, ya ce taron bitar ya samu halartar kwararru na gida da na waje akan batutuwan da suka tattauna, kuma za su mikawa majalisar tarayya rahoton su game da shirin zaben 2023.