✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jana’izar Ariel Sharon: Wasu na kuka, wasu na murna

kasar Isra’ila ta yi wa tsohon Firayiministanta, Ariel Sharon jana’izar ban girma, inda al’umamr kasar da abokan huldarsa suka nuna alhini, yayin da wasu Falasdinawa…

Marigayi Ariel Sharonkasar Isra’ila ta yi wa tsohon Firayiministanta, Ariel Sharon jana’izar ban girma, inda al’umamr kasar da abokan huldarsa suka nuna alhini, yayin da wasu Falasdinawa suka yi murna. Mataimakin Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi jawabi a gaban tutar da ke kadawa a kan makararsa, inda ya bayyana shi a a matsayin gwarzo, mayaki mara tsoro.
Sharon ya mutu yana da shekara 85. Shi ne dai shugaban Isra’ila wanda kimarsa ta raba kan al’umma, domin ya rike mukamai a aikin soja, inda daga bisani ya tsunduma cikin harkokin siyasa, sannan ya shawo kan abin kunyar da ya aikata, har ya kai ga zama Firayiminista. Marigayin ya shafe shekara takwas yana fama da ciwon shanyewar gabban jiki.
Ariel Sharon ya shafe tsawon rayuwarsa yana yaki da Larabawa, wadanda suka zamar masa makiya, sannan ya yi kokari wajen daukaka darajar Yahudawan Isra’ila. Sai dai wani abin mamaki da ya aikata shi ne yadda ya janye sojojin Isra’ila daga zirin Gaza a shekarar 2005, tare da janye ’yan kama wuri zauna, bayan sun shafe shekara 38 a wurin.
Shugaba Shimon Prese, tsohon abokin marigayin, wanda kuma ya taba zama abokin hamayyarsa, ya yabe shi, inda ya bayyana shi a matsayin ‘zaki.’ Shi ma Firayiminista Netanyahu, wanda ya yi murabus daga Gwamnatin Sharon, don nuna rashin amincewarsa da janyewar Sharon daga zirin Gaza, ya bayyana shi a matsayin babban mayaki.
Tasohon shugaban Birtaniya, Mista Tony Blair ya halarci jana’izar Ariel Sharon, inda ya yabe shi. Ita ma kasar Jamus ta aike da wakilai.
Su kuwa bangaren Palasdinawa, sun harba roka a saitin gonar da aka binne Sharon, a Kudancin Isra’ila, don yin tuni kan halin matsalar tsaro da aka fuskanta a zirin Gaza. Kodayake dai makamin da suka harba bai shiga cikin Isra’ila ba.
kasar Masar ma ta aike da jami;/an difulomasiyyarta, kamar yadda ofishin jakadancinta ya nuna