✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jaridun Daily Trust sun taka rawar gani – Umaru Dembo

 Mene ne tarihinka?  Ni Alhaji Umaru Dembo yau ina da shekara 73 a duniya, na koyi aikin jarida a birnin Landan, na yi aiki da…

 Mene ne tarihinka? 

Ni Alhaji Umaru Dembo yau ina da shekara 73 a duniya, na koyi aikin jarida a birnin Landan, na yi aiki da Kamfanin Watsa Labarai na Arewa (NBC) wato gidan Rediyon Tarayya na Kaduna a yanzu sannan na koma aiki a kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo a Kaduna. Daga nan na yi ritaya na tsunduma harkar buga jarida mai zaman-kanta da litattafai. Na lura Cif MKO Abiola na da jarida mai zamn kanta a Kudu, Cif Aled Ibru na kare gabashin kasar nan, sai ni kuma na bude Teled da Zuma da Hantsi don kare Arewa da kasa baki daya. An kaddamar da jaridar “The Teled” ta Ingilsihi da Zuma ta Hausa ne a Zariya a 1980 a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Neja na wancan lokaci wanda kuma a yanzu shi ne Sarkin Suleja, Alhaji Awwal Ibrahim. Daga baya na kafa kungiyar kwallon kafa ta Teled, Zariya. Na halarci taron gyara tsarin mulki  a 1985. Na halarci cibiyar horar da nazarin bukatu ta kasa da ke Kuru a 1990. Na tsunduma cikin siyasa gadan- gadan inda na yi takarar neman zama Gwamna a inuwar Jam’iyyar NRC. Duk a lokacin ina buga mujallu amma cikin matsi don siyasar Najeriya sai da kudi. Na zama Minista a Ma’aikatar Man Fetur a zamanin Janar Sani Abacha a 1998.  A yanzu kuma ni ne Babban Daraktan kungiyar Tallafa wa Janar Buhari wacce a ake kira BSGC da ke Abuja da mabiya a fadin kasar nan. 

 Yaushe ka fara dab’i?

 Na fara lokacin da akwai gwabi, domin ijunan aiki da takardu da wutar lantarki da man dizal ba su da tsada. Bugu da kari ana da son karatu kuma ana sayen mujallun don Naira tana da karfi sosai kafin a tilasta wa Najeriya tsarin jari-hujja na SAP da dora wa jama’a bakar fatara da suka kasa biyan bukatun kansu balle su sa yi mujalla ko jarida.

 Wadanne matsaloli ne suka janyo ka daina buga jaridas da mujallu?

 Darajar Naira ta fadi, shigo da injin dab’i na zamani don inganta aiki ya kara tsada, kula da madabba’a ya kara wuya, dauka da biyan ma’aikata ya zama alakakai, ga rashin tallafi na aikin buga litattafai da yin tallace-tallace daga gwamnoni da daidaikun manyan kamfanonin da ke Arewa, ga sayen man gas, ga rashin cinikin mujallun, ga shari’a daban-daban a kotuna game da wadanda suke zargin an ci mutuncinsu, ga biyan kudin lauyoyi, ga rashin wutar lantarki tsayayyiya, ga walahar aiki karkashin mulkin soja.

Ababen suna da yawa, gwamnati ba ta tallafawa, duk tonon silili na bin kwakkwafi da dan jarida ya yi, soja suna yin bita-da-kulli da salo iri-iri, ga durkushewar kamfanonin sarrafa takardun da ake buga jaridu da sauransu, fatara da taulauci sun rage kasuwar saboda SAF, da SFEM da sauransu. Rediyo na da arha bisa sayen jarida ko mujalla, don da an sa batir shi ke nan. Kuma gwamnatocin baya kafin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci zabe, ba su damu talaka ya san abin da suke yi ba, don sun fi son yin dabaru da yin rub-da-ciki. Ga sauya kayan aiki da sababbi na zamani na da tsada ga kuma uwa uba harkar tsaro. Da muka dan tsayar da aiki, kafin mu ci gaba da aiki, sai barayi suka yi ta sace kayayyakin aikin. 

A matsinyinka na tsohon mawallafi me za ka ce game da cika shekara 20 da kafa kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya?

 Ina matukar jinjina wa wadanda suka kafa wannan kamfani da ya cika shekara 20 don suna aikin gina kasa da kare martabar Arewa da aiki da bangarori da dama cikin yanayi mai saurin sauyawa. Ya dace gwamnati da rika tallafa wa masu wallafa jaridu don darajar Naira da ake amfani da ita, domin sayo kayayyakin aiki daga kasashen waje na cikin yanayi mai wuya. Ba kasar da za ta ci gaba idan mutanenta ba sa yin karatu. Yanar gizo na da alfanu amma da matsaloli, domin yara sun fi son kallace-kallace maimakon amfani da su don kara ilimi, tsadar kudin man dizal yana yi wa harkar dabaibayi. Masu buga mujallu da jaridu da masu gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu ba sa samun fitar da uwar-kudi ballantana riba. Ya dace a tallafa musu don suna daukar ma’aikata da rage zaman kashe wando. A yau gigajen buga jaridu na gwamnati guda nawa ne suke aiki?

 A matsayinka na tsohon Ministan Man fetur, yaya za a yi mai ya wadata a kasar nan?

Ba mu san abin da ake ciki ba don muna daga waje, amma mun san mun yi yunkurin gyara da kafa wasu lokacin muna gwamanati, kafin Janar Sani Abacha ya rasu, sai aka yi watsi da tsarinmu, abin da wuya sosai domin ana fitar da kudi amma gaskiyar ita ce, a gyara wadanda muke da su, sannan kuma a gina wasu sababbin matatu.

Kuma muna murna da matatar mai da Alhaji Aliko dangote yake ginawa a Ikko, da fatan abin ya dore.