✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarirai uku suka mutu a layin karbar fom din tallafi

An matse jarirai guda uku wanda ya yi sanadin rasa rayukansu a turmutsutsun layin karbar fom din shirin tallafin noma da kiwo na hadin gwiwar…

An matse jarirai guda uku wanda ya yi sanadin rasa rayukansu a turmutsutsun layin karbar fom din shirin tallafin noma da kiwo na hadin gwiwar Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya da Kungiyar APPEALS a harabar ofishin shiyya na Hukumar Bunkasa Harkokin Noma ta Jihar Kaduna da ke garin Sabon Birni a Karamar Hukumar Lere, a makon da ya gabata.

Shi dai wannan karbar fom na tallafin noma da kiwo na APPEALS da wannan al’amari ya faru ya tara dubban mutane maza da mata daga garuruwa da kauyuka na kananan hukumomin Kubau da Kauru da Lere wanda ya kawo cunkuso a wajen.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani kan wannan al’amari, daya daga cikin wadanda suke bayar da tsaro a wajen kuma ma’ajin kungiyyar ’yan sintiri na Karamar Hukumar Lere Malam Aliyu Yahaya ya bayyana cewa yanayin cunkoson jama’a ne ya sa aka samu wannan matsala, wanda ya kai ga rasa rayukan jirirai guda uku, da wata mata da ta suma.

Ya ce wadanda suka rasu din jirarai ne da ake goyansu. Kuma sun rasu ne sakamakon layin da matan suka yi, inda aka matse masu goyonsu har suka mutu.

‘’Mun yi ta cewa matan kowace mata ta kwance goyon ta ta rike a hanu saboda gudun faruwar wannan al’amari, amma wasu matan suka ki jin maganarmu. Har aka kai ga matse wadannan yara suka mutu. Farko a shekaranjiya guda biyu suka rasu, washegari kuma guda daya ya rasu. Sai wannan mata da ta suma sakamakon wannan cunkoso da zafi.”

Ya ce wannan shiri na mata da maza ne, amma sai mata suka fi yawa a wajen domin mata daga garuruwa da kauyuka daga ko’ina a kanannan hukumomin Kauru da Kubau da kuma nan Lere ne suka halarci wannan waje,  domin karbar wannan fom na tallafin noma da kiwo.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin jami’an da suke gudanar da wannan shiri da aka turo, kan wannan al’amari amma sunki yin magana.