Da Dumi Dumi

Jibi za a kaddamar da Gidauniyar Cibiyar Sheikh Sharif Saleh

A jibi Lahadi ne za a yi bikin kaddamar da Gidauniyar Cibiyar Sheikh Sharif Saleh da (Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Islamic Centre – SHISIC) a Abuja. Taron kaddamar da gidauniyar zai gudana ne a karkashin shugabancin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, a dakin taro na  Kasa (International Conference Center) da ke Abuja. Babban mai kaddamarwa shi ne Alhaji Abdussamad Isyaku Rabi’u, Shugaban Rukunin Kamfononin BUA, yayin da ake sa ran halartar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da ministoci da manyan ’yan kasuwa da ’yan siyasa.Daga cikin abubuwan da cibiyar za ta kunsa akwai masallaci da dakin taro da dakin karatu da ajujuwa da studiyo da wajen atiysaye da dakunan kwana da karamin asibiti da wajen cin abinci da kuma wajen ajiye motoci.

Za a fara taron ne da misalin karfe 9 na safe.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya