✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jigawa za ta fara biyan albashin Naira dubu 30 a wannan wata

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya ce gwamnatinsa za ta fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30 a wannan wata na…

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya ce gwamnatinsa za ta fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30 a wannan wata na Oktoba.

Gwamna Badaru Abubakar ya bayyana haka ne a wajen bikin Ranar Malamai ta Duniya da aka gudanar a Dandalin Malam Aminu Kano da ke Dutse a ranar Asabar da ta gabata.

Gwamna Badaru ya ce tuni ya kafa kwamatin duba yadda tsarin biyan albashin zai kasance kuma shi ne shugaban kwamitin. Ya hori ma’aikata su guji sakaci da aiki kuma ba zai amince da wasa da aiki ba. Ya ba malaman tabbacin samun mafi karancin  allbashi na Naira dubu 30 daga watan Oktoban nan.

Tun farko Shugaban Kungiyar Malaman Makaranta (NUT) ta Jihar, Kwamared Abdulkadir Yunusa Jigawa ya  roki Gwamnatin Jihar  ta biya ma’aikata albashi mafi karantanci na Naira dubu 30 musamman malaman  makaranta.