Gwamnatin Jihar Jigawa ta kebe kananan hukumomi 22 daga cikin 27 na jihar don gina musu ban-dakuna da nufin inganta tsabtar muhalli tare da daura damarar yaki da ba-haya a fili.
Shugaban Hukumar Tsabtace Ruwan Sha da Muhalli ta Jihar Jigawa Malam Labaran Adamu Hadeja ne ya tabbatar da haka, inda ya ce gwamnati ta fito da tsarin gina ban-dakin ne a yankunan karkara inda a can ne magidanta da dama ba sa iya samar da ban-daki a gidajensu. Ya ci gaba da cewa Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Asusun UNICEF da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Jigawa ne suka dauki nauyin aikin. Ya kara da cewa za a samar da irin wadannan ban-dakuna a makarantu da asibitocin jihar don ganin an kare muhalli daga gurbacewa.
Malam Labaran ya kara da cewa yanzu haka gwamnatin jihar ta gina ban-daki 2000 a kasuwanni da asibitocin jihar.
A bangaren samar da tsabtataccen ruwa sha a yankunan karkara kuwa, ya ce gwamnatin jihar ta gina tuka-tuka 2,500 a kokarin gwamnatin jihar na samar da ruwan sha mai tsabta.