✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin sama ya kashe mutum biyu a Legas

Masu ba da agaji na aikin ceto bayan girgin saman ya rikito a cikin wani gida a ranar Juma'a

Hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu ya yi sanadiyyar mutuwar da wasu mutum biyu tare da jikkata wani a jihar Legas.

Rahotanni na cewa jirign ya rikito daga sama ne ya fado a wani gida a layin Salvation Road a yankin Opebi.

Kakakin Hukumar Agaji ta Jihar Legas (LASEMA), Nosa Sokumba ya tabbatar da aukuwar hatsarin na ranar Juma’a wanda ya rutsa da jirgin kamfanin Quorom Aviation.

“Tabbas jirgi mai saukar unugulu ya fado da misalin 12 na rana a Opebi. Jami’an LASEMA na kokarin ba da agaji a wurin”, kamar yadda aka ruwaito shi.

Janar Manajan Hukumar Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce an garzaya da mutumin da ya samu rauni daga hatsarin jirgin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas.

“An yi wa hukumar kiran gaggawa cewa wani jirgi mai saukar ungulu na haya ya fada cikin wani gida …nan take muka fara shirin bayar da agaji.”, inji shi.

Karin bayani na tafe…