✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Jirgin yaki ya hallaka ’yan fashi a Kaduna

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kashe ’yan fashi a yayin da suke kokarin satar shanu a yankin Kuzo da ke Jihar Kaduna. ’Yan fashin…

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kashe ’yan fashi a yayin da suke kokarin satar shanu a yankin Kuzo da ke Jihar Kaduna.

’Yan fashin wadanda suke wani fili a yankin Gabas maso Yammacin dajin, an kashe su ne bayan jirgin yakin rundunar ‘Operation Thunder Strike’ ya yi musu luguden wuta.

Shugaban Sadarwa na Rundunar Tsaro ta Najeriya, Manjo Janar John Enenchea cikin wata sanarwa ya ce helikoftan soji da ke sintiri a yankin ne ya hallaka ’yan ta’addan.

Sanarwar ta ce, “Mayakan sama na Operation Thunder Strike sun kashe ’yan bindiga da dama a yankin Kuzo da ke Jihar Kaduna, yayin da suke yunkurin safarar dabbobin da suka sata ta yankin” inji shi.