✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ka nazarci rahoton kwamitin kafin fara aiwatar da komai a Gombe – Sanata Lidani

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe na farko a mulkin farar hula a karkashin jam’iyyar ANPP kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta Kudu, Barista Joshua Moljokob…

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe na farko a mulkin farar hula a karkashin jam’iyyar ANPP kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta Kudu, Barista Joshua Moljokob Lidani, wanda har ila yau shi ne Shugaban Kwamitin mika mulki ga sabuwar gwamnati ta Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, na jam’iyyar APC, ya bai wa sabon Gwamnan shawarar cewa ya nazarci rahoton kwamitin mika mulki kafin fara aiwatar da komai saboda akwai lauje cikin nadi. Ga yadda tattaunawarsa da Aminiya ta kasance.

A matsayin ka na Sanata kuma shugaban Kwamitin mika mulki ga sabuwar Gwamnati ya za ka bayyana ci gaban da ka gani a jihar Gombe?

Eh, gaskiya an samu ci gaba tun daga lokacin mulkin mu na farko na Alhaji Abubakar Habu Hashidu, a ANPP zuwa Danjuma Goje, har zuwa kan shi Ibrahim Hassan Dankwambo da yake shirin barin gado a Yan kwanaki masu zuwa, da Inuwa Yahaya zai karba shi ma ya yi kokarin sa.

Jihar Gombe tana tsakiyar jihohi 6 na arewa maso gabas, ya yanayin tsaro anan Gombe?

Jihar Gombe akwai zaman lafiya kowa yana mutunta kowa hakan ya sa ta zaman abun koyi ga sauran jihohi da suke kewaye da ita har ake sha’awar jihar wasu ke dawo wa su zauna.

Duk da cewa akwai zaman lafiya kwanaki an samu hatsaniya inda wani jami’in tsaro ya kashe Yara 9 ya aka shawo kan lamarin?

Saboda kowa yasan ba halin yan Gombe bane tashin hankali kuma na gaya ma kowa yana mutunta kowa a jihar hakan yasa aka zauna aka tattauna aka fahimci juna cikin lumana saboda ba’a san yan Gombe da tashin hankali ba, da kuma hadin kan manyan gari da masu fada aji.

A lokacin kuna mulkin a shekarar 1999 kune silar fara kawo ci gaba na ayyukan raya kasa a Gombe kuma kace sauran gwamnonin ma sun kamanta to wane kira kake da shi ga Inuwa Yahaya akan haka?

Na san Gwamna Inuwa Yahaya mutum ne haziki mai kokari, zai kuma yi kokari saboda yana da kishin jihar Gombe da mutanen ta, sannan kuma zai hada kan mutanen Gombe dan a ci gaba da zama lafiya, zai kuma yi abun da mutane ba su yi tsammani ba saboda jihar ta ci gaba da zama sahun farko a arewa maso gabas na kasar nan.

Ganin kai ne shugaban kwamitin mika mulki ga sabuwar Gwamnati a ranar 29 ga watan nan na mayu wane shawara za ka bai wa Inuwa Yahaya a bangaren da zai fi mayar da hankali?

JHaka ne ganin ina cikin kwamitin da Gwamna ya nada na mika mulki, da muka mika rahoto a ranar asabar din da ta gabata akwai shawarwari da yawa da aka ba shi a kwamitance, amma munyi tafiya tare tun lokacin yakin neman zabe nasan ya yi alkawura da dama kuma yana hawa mulki zan dinga tuna masa lokaci zuwa lokaci duk da ma nasan zai iya cika alkawari dan Inuwa mutum ne mai fada da cikawa.

A Jihar Gombe a gwamnatin da ta gabata, ta Goje, mata masu ciki suna samun magani Kyauta a asibitocin gwamnati  har zuwa haihuwa, idan Tiyata ma ta kama, za’a yi duk kyauta ne, amma yanzu an dai na, wannan shiri, wacce Shawara za ka bai wa shi Gwamna mai jiran gado idan aka rantsar da shi.?

Zai yiwu ya dawo da tsarin, zai iya yiwuwa, kuma sai ya duba domin akwai kura a wannan gwamnatin ta Ibrahim Dankwambo domin ya bar dimbin basussuka, shi yasa na ba shi Shawara da cewa ya bibiyi rahoton kwamitin a hankali, kar ya yi sauri, kafin fara aiwatar da komai.

Har ila yau a Jihar Gombe akwai matasa masu yawa da basu da aikin yi, duk wani ta’addanci kuma da Matasan ake yi wanne hanyoyi Inuwa zai bi, dan samar musu da ayyukan yi?

Matsalar Matasa tana daya daga cikin abun da Gwamna Inuwa Yahaya zai fara waiwaya, dan tun lokacin da muke yakin neman zabe, yasan akwai wannan matsalar ta rashin aikin yi ga, matasa kuma zai magance ta Insha Allahu.

Ganin Gombe jiha ce da take da Manoma, ake alfahari da ita wajen Noma wane mataki ne Gwamna Yahaya, zai dauka wajen samar da taki akan lokaci?

Tabbas Gwamna yace zai yi dukan mai yiwu wa wajen ganin an samar wa  manoma takin zamani mai kyau mai arha a kan lokaci, ba sai damuna ta wuce sannan a kawo taki ana rabawa manoma ba.

Ko kana da wata shawara ta daban ga shi zababben Gwamna?

Shawarar ita ce ya tsaya ya duba abubuwan da ya gada ya nemi shawarwarin masana da ra’ayoyin mutanen Gombe, akan hanyar da ya kamata abi dan shawo kan matsalar sannan kuma ya rinka sauraran koken talakawa da sauran al’ummar gari, hakan zai taimaka masa wajen sanin wasu abubuwan da yadda zai hada kai da gwamnatin tarayya tunda yanzu jam’iyyar sa da shugaban kasa daya ce, zai iya amfani da damar wajen samar wa da jihar Gombe ayyukan raya kasa.