Search
Subscribe
Kada a bari mafarkin Mambilla ya shiriri ce

Kada a bari mafarkin Mambilla ya shiriri ce

A lokacin da Gwamnatin Tarayya ta sanar da sahale aikin samar da wutar lantarki na Madatsar Mambilla – fiye da shekara biyu – da dama ’yan Najeriya sun yi zaton gwamnatin Buhari ta kawo karshen batun nan na samar da lantarki da ya shafe shekaru aru-aru yana yana ci wa kasar nan tuwo a kwarya. Fiye da shekara biyu kuma har yanzu a lissafi ake, ba a iya kai ko da na’ura guda ba ga kuma rashin biyan diyyar filaye, dadin dadawa ga rashin himma kan aikin daga bangaren gwamnatin China – wacce za ta samar da kashi 85 cikin 100 na aikin. Lura da haka ba za a yi azarbabi ba idan aka ce aikin zai fuskanci matsalar  susucewa baki daya. Cikin wata makala domin murnar amincewa da tunkarar aikin gadan-gadan da Majalisar Zartarwa ta Kasa ta yi fiye da shekara biyu baya, Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, ya ce “Gwamnatoci da dama sun yi yunkuri, ko kuma fadin abin yadda yake sun yi ‘alaye’ cewa sun dukufa wajen tabbatar da aikin, amma ina ba su iya tabuka komai ba.”

Ya ci gaba da cewa: “Yunkuri mai cike da abin kunya na a fara Ginawa da Sarrafa shi tare da Mika shi ga Najeriya (BOT) shi ma ya gaza ko da kuwa a matakin fara aikin.” A takaice dai, bayan amincewa da aikin da Majalisar Zartarwar ta yi a ranar 30 ga Agustan 2017, Kakakin Shugabn Kasar ya kira aikin na Mambilla a zaman ‘Gagarumin Aikin Buhari.’ Koda yake, ba Garba Shehu ba ne kawai ya yi murna a lokaci, a’a shi ma Ministan Makamashi, Ayyuka da Muhalli a lokacin, Babatunde Raji Fashola, ya nuna murnarsa game da aikin, inda ya ce “Zai yi tasiri sosai wajen kawo sauyi a dukkan bangarorin ci gaban tattalin arziki. A lokacin aikin da bayan kammala shi da fara aiki da shi, zai yi tasiri mai ma’ana ta fuskar raba wutar lanatrki da ayyuka da samar da ayyukan yi da yawon bude-ido da yada fasaha da ci gaban karkara da noman rani da kuma uwa uba samar da abinci a yankin da ma wasu wuraren.”

Domin soma aikin, Fashola ya rattaba hannu kan kwangilar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma wasu kamfanoni uku na China a ranar 10 ga Nuwamban 2017. A wajen sanya hannu kan kwangilar, Ministan ya ce: “Aikin ya zama tamkar sabon babi ne ga raba hannu ta fuskar samar da makamashi a Najeriya daga bangarori daban-daban. Aikin zai kuma ba mu damar aminci a harkar makamashi; zai kuma ba mu damar dabbaka yarjejeniyar Paris kan Sauyin Yanayi – sakamakon yadda zai ba mu damar yin amfani da makamashin da ake sake sarrafa shi.”

Lallai haka yake, aikin ya zama wanda ba ya da na biyu a Najeriya. Tsarin kwangilar ya hada da gaggan madatsun ruwa hudu da wasu dakunan samar da lantarki guda biyu a karkashin kasa masu bangarorin 12 da kowanensu zai bayar da Megawatt 250. Ya kuma hada da layukan lantarki masu karfin KB 330 masu tsawon kilomita 700 daga Makurdi zuwa Jalingo. Sai kuma hanyoyin mota masu tsawon kilomita120 da za su hada yankin da ake aikin da sauran yankunan da ke kusa tare da sake tsugunar da al’ummomin da aka kiyasta yawansu ya kai dubu 100.  Jimillar kudin da aikin zai lashe ya tasam ma Dalar Amurka biliyan shida (Dala biliyan 5 da miliyan 792 da dubu 497da 62). Aikin gina tashar zai dauki tsawon wata 72 ko shekara shida kuma kamfanonin kasar China uku ne za su yi aikin da suka hada da – China Gezhouba Corporation (CGCC) da Sino Hydro Corporation Limited da kuma CGOCC. Bankin China EdimBank kuma zai samar da kashi 85 cikin 100 na kudin da ake bukata yayin da Najeriya za ta biya kashi 15. Idan aka kare aikin, tashar lantarkin Mambilla za ta samar da wuta mai karfin Megwatt 3050 – kuma za ta dara wutar lantarkin da dukkan tashoshin samar da makamashin da ake da su a yanzu na Kainji da Jebba da Shiroro da Zungeru da Gurara da  Kashimbilla da kuma Dadin-Kowa. Daga irin abin da zai faru, a fili yake cewa aikin na Mambilla wani muhimmi ne da zai iya taimaka wa kasar nan wajen ’yantuwa ta bangaren bukatunta na makamashi.

Har ila yau wani mataki ne na dabarun amintar da kasar nan wajen raba kafa ta fuskar samar da makamashi musamman bayan jarraba hanyar samun lantarkin daga iskar gas wadda take tattare da matsalolin da suka hada da saukin yi masa kafar ungulu ta hanyar katse turakar iskar gas din da kuma yadda ake samun kiki-kaka a tsakanin Kamfanin NNPC da kamfanonin samar da lantarkin. Shiri da Dabarun Tsaro/Amintar Kasa da Shugaba Buhari ya kaddamar makonni kalilan da suka wuce ya yi bayanin haka yadda ya dace, inda a ciki ya ce: “Samar da makamashi muhimmi ne a fagen habaka tattalin arziki da ci gaban Najeriya. Allah Ya albarkaci kasar nan da arzikin mai da iskar gas da ruwan koguna da iska mai karfi da kuma hasken rana: Sai dai kash! Ba ta kasance tana samarwa tare da rarraba lantarkin ba wadda za ta dafa wa zaburar da tattalin arzikin kasar ba.”

Tabbas babu wani ci gaba in ma na masana’antu ne ko na daban da zai samu ba tare da ingantaccen makamashi abin dogaro ba – haka batun yake ga bangaren kanana da matsakaitun masana’antu. Manyan kamfanoni kamar na hada motoci da sauransu – za su iya aiki ne kawai idan akwai lantarki abin dogaro kuma mai rahusa. A bayyane yake cewa Najeriya fa ba za ta taba ci gaba a fannin masana’antu ba ta amfani da janaretoci. Muna kira ga gwamnatin Buhari ta cika alkawuran da ta dauka kan wannan aiki – domin kada ta bi sahun gwamnatocin da suka gabace ta – da suka gagara tabbatar da aikin a zahiri.

Aminiya tana cike da farin cikin cewa aikin na Mambilla yana daya daga cikin muhimman ayyukan da gwamnatin Buhari za ta bai wa fifiko a wannan shekara. A budaddiyar wasikarsa ga ’yan Najeriya a shafukan da dama na jaridun kasar nan a ranar 1 ga Janairun bana, Shugaba Buhari ya ce za a fara aikin na Mambilla a rabin farko na bana. Yayin da muke da kwarin gwiwa kan wannan ikirari, muna kuma kiransa da kada ya tsaya ga magana kawai, a’a ya kamata ya kafa hukumar tabbatar da an gudanar da aikin kan lokaci wanda zai shawo kan duk wani kalubalen da ka iya kawo cikas ga aikin, wajen ganin an fara aikin kuma ya zama yana yi wa Shugaban Kasa bayani kan ci gaban aikin a duk mako. Ya nada Mataimakinsa ya zaman Shugaban hukumar tare da Ministan Makamashi da Gwamnan Jihar Taraba da wadansu jiga-jigan gwamnati a matsayin mambobin hukumar – domin su tabbatar da an shawo kan dukkan matsalolin da ke kawo tarnaki wajen aikin kamar rashin himmantuwa wajen fara aikin daga banagaren China cikin gaggawa.

Akwai kuma bukatar a fito baro-baro wajen tabbatar wa China za a warware dukkan koke-kokenta dangane da aikin, kamar na batun cewa za a biya ta rancen tare da dorewar aikin. Idan ma ta kama, Najeriya ta samar da asusu na musamman da za ta zuba kashi 15 na kudin aikin daga bangarenta – domin nuna cewa gwamnati a shirye take wajen fara aikin. Biyan diyya ga al’ummomin da ke zaune a yankin da aikin yake – shi ma wani bangare ne da ya kamata a tabo wajen tabbatar da an soma aiwatar da aikin ba tare da wata matsala ba. Idan ya zama lallai, ya kamata a tunkari batun daga dukkan bangarorin gwamnatoci na tarayya da ta jiha da kuma ta karamar hukumar da abin ya shafa wajen ganin sun saka ido sosai kan gagarumin aikin da zai samar da karin wutar lantarki ga kasar nan. Idan ya zama tilas, Bangaren Zartarwa da na Majalisar Dokoki da sauran wadanda suke da ruwa-da-tsaki a batun, akwai bukatar su hada karfi da karfe waje domin nuna himmarsu game da wannan gagarumin aiki da zai samar da karin wutar lantarki da kasar ke matukar yunwarta.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin