Da Dumi Dumi

Kafafen Sadarwa: Majalisa ta gabatar da kudurin daurin shekara 3  

Majalisar Dattawan Najeriya ta sake dawo da kudirin da zai tsaftace Kafafen Sadarwar Zamani a Najeriya. Wannan  kudirin dokar zai tanadar da daurin shekara uku a gidan yari ga duk wanda taka dokar ta aka gindaya.

A cewar Majalisar wannan kudiri zai taimaka wajen yakar yada labaran karya a shafukan yanar gizo da  shafukan sada zumunta a Najeriya. An dai gabatar da wannan kudiri a zauren majalisar a karon farko a zaman Majalisar Dattawan ranar 6 ga watan Nuwamba, 2019. Kudirin dokar yana cikin kudirori 11 da aka yi zama a kansu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya