✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kaka ya yanke shawarar zama a kulob din Real Madrid

Ricrado Kaka, dan asalin Brazil da yanzu haka yake wasa a kulob din Real Madrid ya ce ya yanke shawarar cigaba da zama a kulob…

Ricrado Kaka, dan asalin Brazil da yanzu haka yake wasa a kulob din Real Madrid ya ce ya yanke shawarar cigaba da zama a kulob din a kakar wasa ta bana musamman ganin yadda tsohon kocinsa a kulob din AC Milan Carlos Ancelotti ya karbi ragamar kulob din daga Jose Mourinho.
Shi dai dan kwallon a ’yan shekarun baya an rika alakanta shi da barin kulob din ne zuwa wasu ganin yadda tsohon koci Mourinho yake yawan ajiye shi a benchi.
Kaka, dan shekara 31, ya ce zai tattauna da sabon kocin kulob din ne don gann yiwuwar ya cigaba da zama a kulob din.
Idan za a tuna sabon kocin Madrid, Carlo Ancelotti ne ya sayo Kaka daga kulob din Santos da ke Brazil a lokacin da yake horarwa a kulob din AC Milan a shekarar 2003 amma daga baya Madrid ta saye shi daga Milan a shekarar 2009.