✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kalankuwar fina-finai ta Cannes: Yadda karrama fim din badala ta haddasa tarzoma a Faransa

A Lahadin da ta gabata ce aka rufe kalankuwar fina-finai ta duniya mai taken ‘Cannes Film Festibal 2013’ wacce aka gudanar a kasar Faransa.Kalankuwar, wacce…

A Lahadin da ta gabata ce aka rufe kalankuwar fina-finai ta duniya mai taken ‘Cannes Film Festibal 2013’ wacce aka gudanar a kasar Faransa.
Kalankuwar, wacce ita ce karo ta 66 da aka gudanar, ta haifar da rudani, inda wani fim na badala ya samu babbar kyautar karramawa. A yayin rufewar ne aka zabi fim din ‘Blue is the Warmest Colour’ wanda wani mai bayar da umurni a fina-finai, dan kasar Tunisia, Abdellatif Kechiche ya shirya, aka yi masa karramawa ta musamman a matsayin fim din da ya yi fice daga fina-finan da aka gabatar.
Fim din, wanda Adele Edarchopoulos da Lea Seydoud ke jagorantar sauran ’yan wasa a cikinsa, an shirya shi ne daga labarin soyayya, kamar yadda yake a littafin Julie Maroh.
Fim din na dauke da labarin wata budurwa ce da ta kamu da son wata mata, wacce ta dan grime ta kadan. Yana bayyana yadda soyayyar mace da mace ke kasancewa, wadda haka ta haifar musu da la’antattar dabi’ar nan ta madigo.
Ba a jima da bayyana zaben wannan fim a matsayin gwarzo ba, sai al’ummar Faransa, musamman masu ra’ayin ’yan mazan jiya suka kwarara a titunan birnin Paris suna zanga-zangar nuna adawa da la’antar wannan hukunci. Haka kuma, dama tun farko a makon jiya ne aka zartar da dokar da ke ba al’ummar Faransa ’yancin auren jinsi daya. Dalili ke nan masu adawa da wannan doka suka alakanta karrama wannan fim da ita dokar, wanda haka ya sanya suka nuna bacin ransu. An samu bayanin cewa sama da mutum 150, 000 suka shiga cikin wannan zanga-zanga.
Baya ga fim din na badala, sauran wadanda suka samu kyautar karramawa a kalankuwar ta Cannes sun hada da fim din ‘Inside Llewyn Dabis’ wanda ’yan uwa Coen Brothers suka bayar da umurninsa. Haka kuma fim din ‘Like Father, Like Son’ na darakta Hirokazu Kore-Eda, dan kasar Japan ya samu kyauta. Haka shi ma fim din ‘Heli’ na dan kasar Medico, Amat Escalante, ya samu kyautar gwarzon darakta.