✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kananan ‘yan kasuwa na taka rawar gani a ci gaban tattalin arzikin kasa – Osinbajo

Maitaimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana gagarumar rawar da kananan ‘yan kasuwa ke takawa wajen habaka tattalin arzikin kasa. Ya ce duba da…

Maitaimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana gagarumar rawar da kananan ‘yan kasuwa ke takawa wajen habaka tattalin arzikin kasa. Ya ce duba da haka ne Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta bullo da tsarin bai wa kananan ‘yan kasuwar bashin Naira dubu 10.

Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne a yayin ziyarar da ya kai a wasu kasuwannin Jihar Legas a ranar Litinin din da ta gabata, ziyarar da ya yi a wasu kasuwannin dake yankin Oshodi da Ketu da unguwar Bariga.

Ya ce izuwa yanzu an kaddamar da tsarin baiwa kananan bashin a jihohi 33 na kasar nan kana mutum dubu 8 sun amfana, “a wannan tsarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bijiro an tsara shi yadda kananan ‘yan kasuwa miliyan biyu zasu amfana” inji shi.

Mataimakin Shugaban ya ce bashi ne da babu ruwa cikinsa kuma ba a bukatar jingina kafin a ba karamin dan kasuwa, kuma ya ce ana biyan bashin ne cikin watanni shida sannan duk dan kasuwar da ya biya bashin Naira dubu 10 zai iya karbar Naira dubu 15.