✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanawa a yi hattara da jifar shugabanni

Al’adar hawan sallah da sarakunan Kano ke gudanarwa a lokutan kowace karama da babbar sallah, ya kasance wani mahimmim bangare a bukukuwan sallah da Kanawa…

Al’adar hawan sallah da sarakunan Kano ke gudanarwa a lokutan kowace karama da babbar sallah, ya kasance wani mahimmim bangare a bukukuwan sallah da Kanawa ke tinkaho da su, kama daga hawan Daushe wanda ake yi a ranar biyu ga sallah a kofar fada da hawan Nassarawa, inda sarki ke kai wa gwamna gaisuwar sallah, a gidan gwamnati sai kuma hawan dorayi da na Fanisau.
A yayin wadannan haye-haye ne sarki ke ganawa da talakawansa tare da yi musu barka da sallah, cikin nishadi da annashuwa da girmamawa, Kanawa na matukar alfahari da wadannan haye-haye. Har ila yau, wadannan haye-haye da ake gabatarwa suna kara kwarzanta masarautar Kano da Kanawa a kan sauran garuruwan kasar nan da ma kasashen waje. Hakan ne ya sa baki na cikin gida da na kasashen waje ke tururuwa domin halartar wadannan haye-haye masu kayatarwa.
Amma kash!  Duk da wannan alfanu da tagomashi da tunkaho da ake yi da wadannan haye-haye, akwai wasu halayya na rashin jin dadi da akasari matasa ke gudanarwa a lokutan da ake gabatar da wadannan haye-haye, inda hakan ke kawo barazana da tarnaki ga kima da tagomashin da kyakkawar manufar da tasa ake wadannan haye-haye a bukukuwan sallah.
Irin wadannan dabi’u na kaico da ke faruwa a lokutan hawa sun faro ne shekaru da dama da suka wuce, inda ake samun barkewar fitina da hayaniya ko tarzoma a tsakanin wasu rukunin da ke cikin ayarin mahayan da kuma wasu jama’a daga ’yan kallo ko mazauna wata unguwa ko kuwa tsakanin tawagar basarake da ta wani basaraken ko kuma tsakanin jami’an tsaro da ’yan kallo, a kokarinsu na ganin al’amura sun gudana cikin kwanciyar hankali da lumana. Irin wannan arangama da ke faruwa kan kai a wasu lokutan ga samun munanan raunuka, inda tsautsayi ma har takan kai ga rasa rai, ga kuma sanya firgici da razana a zukatan sauran ’yan kallo da sauran jama’ar gari.
Masu iya magana sun ce “itace tun yana danye ake iya tankwara shi,’’ rashin daukar wani sahihin mataki wajen dakile ci gaban wannan ta’ada daga bangaren hukumomi da masarauta, yasa wannan al’amari na, rashin kan gado ke ci gaba da faruwa, inda takai a yanzu an samu sabon salo na yin amfani da irin wadannan lokuta domin cin zarafin shugabanni, inda ake samun wasu tsagerun da ke iya tare tawagar gwamna da jami’ansa, tare da yi musu kalaman batanci da ihu kai har takan kai ga jefe-jefe, daga nan wuri ya yamutse a yi ta guje-guje, a karshe a bar mata da yara kanana da sauran masu tsautsayi cikin munanan raunuka. Hakan kuwa ya fi faruwa musamman yayin hawan Daushe, wanda ke daukar dimbin jama’a maza da mata yara da manya.
Abin bai tsaya nan ba, don kuwa irin wadannan fitintinu sun zamo wani yayi, inda a yanzu babu wanda ya tsira, kama daga kan gwamna da sarki da hakimai da masu rike da mukamai na siyasa da sauran su. Hakazalika wannan dabi’a ta jifar shugabanni da tada tarzoma na ci gaba da zama ruwan dare a wannan jiha, don kuwa yanzu takai ba kawai sai a lokutan haye-hayen sallah ake aiwatar wa ba, a’a duk inda za’a gudanar da wani babban taro da shugabanni za su halarta, to sai yadda ta kasance, duk kuwa ta jami’an tsaron da ke kai kawo a wurin.
Abin tambaya a nan shi ne, mece ce manufar daukar irin wannan mataki a kan shugabanni kuma yayin bukukuwan sallah ko wani babban taro? Shin wace riba masu aikata wannan dabi’a ta cin zarafin shugabanni suka ci ko suke ci?  Mece ce riba idan ka yi sanadiyyar jin rauni ko ka firgita dan uwanka da bai ci ba, bai sha ba?  Shin hamayya ko bambancin siyasa kadai ya isa mizanin laifin da za a dauki irin wannan hukunci?  Kawo yanzu wacce biyan bukata aka samu daga shugabannin sakamakon wata jifa ko cin zarafinsu da aka yi?  Ko kuwa ana yin hakan ne domin burgewa ko nuna sabon salon ci gaban zamani, ko kuwa domin morewa ne kawai?  Shin wannan ba yana tabbatar da zunden da ake yi mana ba, cewa Kanawa ba su da gwani?
To koma dai mece ce manufa da dalilin aikata wadannan al’amura na kaico da Allah wadai, abin takaici ne da koma baya ga sanannun kyawawan dabi’u da nagartar da aka san Kanawa da su tsawon lokaci. Haka kuma kara dakushe kima da daraja da mutuncin da Jihar Kano ke da shi ne a idanun duniya.
’Yan uwana matasa da sauran jama’ar gari, ya kamata mu fahimci cewa, ‘cin zarafi ko cin mutuncin shugaba ko tozartashi masifa ce ga al’umma da makomar ta,’ kuma ba burgewa ba ce sakarci da duhun kai ne. Annabi Muhammadu SAW ya yi hani matuka game da cin zarafin shugaba ko tozartashi. Don haka kamata ya yi matasanmu da ma duk wanda ke taka rawa wajen tayar da hankulan jama’a, mu yi karatun ta nutsu, mu fahimci illar da muke yi wa kanmu da kanmu, wajen dakushe daukakar da Allah ya yi wa jihar mu ta mudubin Najeriya, mu yi amfani da ilimi da kyawawan halayen da aka san Kanawa da su, wajen warware dukkan matsaloli da damuwar da ke damunmu cikin ruwan sanyi. Cin zarafin shugabanni ba zai haifa mana da mai ido ba.
Akwai matakai da hanyoyi da dama na masalaha da ake isar da sako a kan duk wata damuwa ko rashin jindadi ga shugaba, ba tare da cin mutuncin kowa ba, a kuma samu biyan bukata. Cikin su akwai rubutaccen sako ko shawarwari ga shugaba kai tsaye, kira da jan hankali ko nasiha ta baka da baka a kafafen yada labarai cikin hikima da ilimi da siyasa, ko ganawa ta gemu da gemu da shugaba, musamman a kungiyance kan wata matsala ko wata bukata ta ci gaba, ba tare da nuna son zuciya ba, akwai kuma matakai na shari’a idan bukatar hakan ta taso, sai kuma matakin kiranye ga zababbun shugabanni ko kawo sauyi da karfin kuri’a. Wannan shi ne wayewa da burgewa da birnanci.
A iya fahimta ta, matakan yin bore da tada tarzoma ga shugabanni  ya fara wuce gona da iri ne tun bayan dawowa mulkin siyasa ta wannan lokacin, to idan kuwa haka ne, akwai bukatar yan siyasar wannan lokaci su fahimci cewa zaman lafiyar al’umma na dindindin shi ne cin nasara da iya shugabanci, tunzura matasa da daure musu gindi don kawo rudani da dagulewar al’amura ga gwamnati, cin amanar al’umma ne wadda babu wata riba a ciki face da na sani da nadama a karshe.
Lallai ne yan siyasa wadanda ke da gwanati da kuma wadanda ke bangaren hamayya, su sanya Jihar Kano a gaba wajen daukar kwararan matakai, domin ganin an dakile kaifin faruwar wannan dabi’ar jifar shugabanni da matasa ke yi, domin ciyar da jihar da al’ummar ta gaba. Lallai shugabannin siyasa su rika tsawatar wa mabiyansu a zahiri, tare da hukunta duk wanda ya ki ji, hakan zai taimaka kwarai wajen kawo karshen wannan matsala.
Haka kuma bangaren masarauta ma nada tata rawar da zata taka wajen tsawatarwa da umartar mahaya da sauran jama’a, domin a rika kai zuciya nesa a duk lokacin da aka ci karo da wani abin rashin jin dadi, kana a dauki matakan ladabtarwa ga duk wanda aka samu da iza wutar tada tarzoma, don masarauta uwa ce ga kowa.
Akwai bukatar jami’an tsaro da su rika amfani da kwarewar da suke da ita wajen hana afkuwar duk wata tarzoma da bore ko tirjiyar jama’a, idan kuma an tsinci kai a irin wannan yanayi to a nuna kwarewa wajen shawo kan matsalar cikin ruwan sanyi, kana masu laifi su fuskanci hukunci na ba sani ba sabo.
Malaman addini da sauran mutane masu kima a idanun jama’a, na da babbar rawar da za su taka wajen ribanya gabatar da nasihohi da jan hankulan matasa ta fuskar addini da shari’a, don karya zuciyar masu sha’awa ko daure gindi ko aikata wannan mummunar dabi’a a tsakanin jama’a.
A karshe ina kira ga masu aikata wannan dabi’a ta jifa da cin zarafin shugabanni, ko kuma ake amfani da su wajen cimma wata bukata, da su ji tsoron Allah, su sani ba mu da wani gari da ya fi Kano, ku sani zaman lafiya da mutunta juna da jama’ar Kano tayi suna a baya shi ne kashin bayan bunkasar arziki da wadatar wannan jiha. Don haka akwai bukatar kauce wa duk wani abu da zai kawo nakasu, tare da dusashewar wannan daukaka da Allah ya yi mana tsawon shekaru. Mu kauce wa duk wani nau’i na cin mutunci ko tozarta shugaba ko yunkurin tada fitina da kawo rudani a cikin al’umma, mu fuskanci kalubalen da ke gabanmu don ciyar da jihar mu da al’ummar mu gaba.
Allah ya sa mu dace, amin.
Nuhu Garba Musa, Phone: 08034463379, E mail: [email protected], Twiter: @garba_nuh