✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano kal-kal: Wasu na yabo wasu na suka

A kwanakin baya ne gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani shiri mai taken ‘Kano kal-kal’ wanda gwamnatin ta ce ta kirkiro shi ne  da…

A kwanakin baya ne gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani shiri mai taken ‘Kano kal-kal’ wanda gwamnatin ta ce ta kirkiro shi ne  da nufin horar da matan jihar a kan harkar kwashe shara.
A karkashin shirin matan za su samu horo kan yadda za su rika bi gida-gida a cikin lungu da sakon jihar suna kwashe shara ta hanyar yin amfani da kananan motoci tare da kai ta inda aka tanada domin hakan.
A cewar Kwamishinar Al’amuran Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar, Barista Zubaida Damakka Abubakar an kirkiro shirin ne don sama wa mata aikin yi ta yadda za su dogara da kansu.
Kwamishinar ta ce ma’aikatarta ta canza salon yadda take tallafa wa mata wajen sama musu abin yi, inda a da take ba su jari, saboda yadda hakan bai haifar da da mai ido ba. “Hakan ya sa gwamnati ta
yanke shawarar gwada wannan sabon shirin, inda aka samo mata 500 daga kananan hukumomin birnin jihar takwas aka horar da su kan yada za su tuka motar kwasar shara inda za su rika bi gida-gida suna kwasar shara tare da kai ta inda aka tanada a kan kudi kalilan,” inji ta.
Kwamishinar ta kara da cewa shirin na Kano kal-kal zai taimaka wa kokarin Huhumar Tsabtace Muhalli ta Jihar (REMASAB) da kananan hukumomi kan ayyukansu na kula da shara kuma zai bunkasa harkar tsabtar muhalli a jihar.
Sai dai a lokacin da gwamantin ke murna da bullo da shirin na Kano kal-kal, wadansu jama’ar jihar na ganin shirin a wani abu ne da ya saba wa al’adun Hausawa da Fulani wadanda su ne akasarin jama’ar jihar, kuma a gefe wasu na ganin hakan da abu ne na kaskantarwa ga mata.
Wani mai suna Malam Auwal Sani ya ce, “Lokacin da na ji labarin kaddamar da shirin a rediyo na yi mamaki, sai na rika tunanin yadda matanmu na Huasawa za su tuka manyan motoci tare da bin gida-gida suna kwasar shara tare da zubar da ita a inda aka tanada, babu shakka wannan abu ne na kaskanci.”
A cewarsa “Ya kamata komai za a yi a duba al’adar mutanen wurin tukun. Al’adarmu ta Huasawa ba za ta karbi wannan ba. Ya kamata gwamnati ta sake tunani ta samo wa matan nan sana’a mai saukin gudanarwa. Me ya sa gwamnati za ta tallafa wa matan ta hanyar kwasar shara? Idan an dubi dabi’ar mace tuka irin wadannan motoci a cikin gari irin Kano mai cinkoso abu ne mai wahala matuka a gare ta.”
Wata budurwa mai suna Samira Ibrahim ta bayyana wa Aminiya cewa “Na ji Gwamnan Jihar Kano yana cewa wai matan da ba su da miji, ta hanyar wannan aiki za su iya haduwa da mazan aure, bai san cewa wannan aiki zai hana mata da yawa daga cikinsu samun mazan aure ba?
Maimuna Sadi cewa ta yi “Shin gwamnanmu ya san mata ababen giramamawa ne da ya kamata a lallaba su? Wannan aiki ba na mata ba ne, haka kuma wulkanci ne ga al’adar Bahaushe. Me ya sa Gwamna ba zai yi koyi da Gwamnan da ya gada ba inda ya rika tallafa wa matan ta hanyar sama musu sana’o’in hannu?”
Binciken Aminiya ya gano cewa mafi yawan matan da aka horar kan koyon tukin motar ba su iya tukin motar ba, lamarin da ya sa mutane ke yi wa shirin kallon abu mai hadari.
A bangaren wadanda suka amfana da shirin kuwa bakinsu har kunne, kamar yadda Aminiya ta tattauna da Amina Salisu wadda ta bayyana cewa shirin zai magance halin fatara da suke ciki. “Ina fari ciki game da yadda aka zabe ni a cikin wadanda za su ci moriyar wannan shiri, yanzu haka na samu horo kan tukin motar ina fatan wannan aiki zai taimaka min wajen kula da marayun ’ya’yana,” inji ta.
Ta ce tuka motar kwasar shara ya fi wa mace amfani a kan ta rika yawon roko ko bara. Kuma ta ce a shirye take ta fuskanci duk wani kalubale a aikin. “Na san cewa da farko akwai wahala, dole mu yi hakuri har zuwa lokacin da mutane za su fahimci lamarin,” inji ta Wata mai suna Hauwa Muhammad Inuwa ta ce shirin yana da amafani matuka kuma ta yi niyyar yin kokarinta wajen ganin ta samu abin dogaro da kanta ta hanyar aikin.
Game da korafin da jama’a ke yi a kan shirin na ‘Kano kal-kal,’ Kwamishinar Mata ta Jihar ta ce wadanda suke korafe-korafe suna yi ne domin ra’ayinsu. “Tuka mota ba abin tir ba ne a al’adar Hausawa, idan dai har mace za ta tuka mota ta kai ’ya’yanta makaranta ko ta je aiki ko kasuwa, ban ga dalilin da za a ce idan ta tuka mota ta kwashe shara ya zama laifi ba,” inji ta.
Ta ce yawancin matan da suka samu wannan tagomashi sun samu amincewar mazaje da iyayensu. Kuma manufar shirin, ba kawai a samar musu sana’a ba ce, ana so ne su zama masu sama wa wadansu abin yi.
Kwamishinar ta ce “Gwamanti ta kashe fiye da Naira miliyan 50 wajen sayo motocin da gyaransu da kuma horar da matan. Kuma baya ga matan 500 akwai wadansu mata 40 da ake shirin koyar da su harkar kanikanci da nufin idan matsala ta samu motocin a kai wa su kanikawan mata su gyara.”
Aminiya ta gano cewa tuni gwamnati ta sayo motoci 50 ta yadda mutum 10 za su rika amfani da mota daya wajen kwasar sharar suna karbar Naira 20 daga kowane gida. Idan an hada kudin matan za su dauki rabi inda za a jiye rabin don gyaran motar.