✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karamar Hukumar Jos ta Arewa ta tara harajin Naira miliyan 19 cikin wata biyu

Sakataren karamar Hukumar Jos ta Arewa kuma Shugaban Kwamitin Tara Kudaden Shiga na karamar Hukumar, Alhaji Shehu Bala Usman ya ce a cikin wata biyu…

Sakataren karamar Hukumar Jos ta Arewa kuma Shugaban Kwamitin Tara Kudaden Shiga na karamar Hukumar, Alhaji Shehu Bala Usman ya ce a cikin wata biyu da fara aikin kwamitinsu ya tara Naira miliyan 19.
Alhaji Shehu Bala Usman ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce lokacin da suka karbi mulkin karamar hukuma, sun fahimci cewa kudaden harajin da ake karba ba a shigar da su inda ya kamata. Kuma ba a jarbar kudaden yadda ya kamata, sannan gwamnati ba ta yi wa al’ummar da suke biyan kudaden harajin aikin komai don inganta jin dadinsu.
Sakataren ya ce “Don haka muka kafa wannan kwamiti na tara kudaden shiga na karamar Hukumar Jos ta Arewa. Kafin mu kafa wannan kwamiti akwai lokacin da aka yi wata uku ana karbar kudin haraji amma Naira dubu 30 ne kawai aka tara.”
Alhaji Shehu Bala ya ce “Amma da aka kafa kwamitin ya kama aiki sai ga shi a cikin wata biyu mun tara Naira miliyan 19. A kasuwanni da wuraren harkokin kasuwanci da masana’antu da makarantu da gidajen mai da muke karbar wadannan kudaden haraji. A duk inda muka je muna nuna wa mutane cewa da wadannan kudaden haraji da suke biya, akwai kaso na musamman da za a yi musu aiki a wurarensu domin ci gabansu da jin dadinsu.”
Ya yi kira ga ’yan kasuwa da masu sauran wuraren da suke biyan kudaden haraji a karamar hukumar, su bai wa kwamiti goyon baya da hadin kai domin karamar hukumar ta samu kudaden shigar da za ta yi wa al’ummar karamar hukumar ayyukan raya kasa.