✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karamar Hukumar Roni ce kan gaba wajen tsabtace muhalli – Salisu Roni

Karamar Hukumar Roni ta ciri tuta wajen tsabtace muhalli tare da samar da ruwan sha mai tsabta a yankunan karkara da nufin inganta lafiyar al’umma.…

Karamar Hukumar Roni ta ciri tuta wajen tsabtace muhalli tare da samar da ruwan sha mai tsabta a yankunan karkara da nufin inganta lafiyar al’umma.

Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Salisu Sani Roni ne ya shaida wa wakilinmu haka a ganawar da suka yi a ranar Litinin da ta gabata a ofishinsa.

Ya ce karamar hukumar ta sa magidanta sun gina ban-daki a gidajensu a kauyuka, a kokarinsu na hana yin bahaya barkatai domin tabbatar da tsabtar muhalli.

Salisu Roni ya kara da cewa ita kuma karamar hukumar ta gina ban-dakuna a daukacin makarantun firamare da Islamiyya da asibitoci manya da kanana da nufin kauce wa yin bahaya a gefen tituna a karamar hukumar.

Da ya juya kan samar da ruwa, ya ce sun gina tuka-tuka 257 a sassan karamar hukumar.

Ya ce Gwamnatin Jihar Jigawa tana tallafa wa karamar hukumar da wasu kudade da suka kai Naira miliyan goma a baya kafin Gwamnatin Tarayya ta fara bai wa kananan hukumomi ’yancin gashin kansu, kuma da kudin ne suka samun damar aiwatar da ayyukan raya kasa.

Saboda haka ya bukaci gwamnatin jihar ta ci gaba da tallafa musu domin a hada karfi a kai ga biyan bukata, “saboda shi aikin gwamnati tamkar aikin gandu ne,” inji shi.

Game da daukar nauyin karatun yara a makarantun sakandare da wadanda suke karatu a manyan makarantun kasar nan da Jihar Jigawa, ya ce karamar hukumar tana kashe makudan kudi wajen tallafa wa matasa.

Ya ce karamar hukumar ta sayi injinan ban-ruwa 18 ta raba wa matasan da suke aikin noman rani da nufin hana matasa tafiya ci-rani a jihohin Kudu tare da magance zaman banza a tsakanin matasan.