✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karfe 10 za a yi jana’izar Sheikh Albani Kuri

’Yan ta’adda sun yi wa Sheikh Ibrahim Musa wanda aka fi sani da Albani Kuri kisan gilla a gidansa

Wasu da ba sani ko su wane ne ba suni yi wa fitaccen malamin addinin Islama a Jihar Gombe, Sheikh Ibrahim H. Musa, wanda aka fi sani da Albani Kuri, kisan gilla.

A cikin daren Talata ne maharan da ake zargin ’yan ta’adda suka kusta gidan malamin a da ke Gombe suka hallaka shi.

Ana sa ran gudanar da jana’izar Sheikh Albani Kuri sa da misalin karfe 1:00 na yau Laraba a Masallacin Juma’a da ke Bolari Gombe.

Sheikh Albani na daga cikin fitatttun malamai da ’yan a’adda suka wa kisan gilla, kamar Sheikh Jaafar Mahmud Adam da kuma Sheikh muhammad Auwal Adam Albani Zariya.