Da Dumi Dumi

Karin albashin da aka yi ya dace a wannan lokacin da ake ciki?

A makon jiya ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar mafi karancin albashi, na Naira dubu 30. Labarin karin ya sanya wadansu cikin murna, musamman wadansu daga cikin ma’aikata, amma wadansu kuma musamman wadanda ba sa aikin wata sun yi tir da karin, inda wadansu daga cikinsu ke cewa zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan lamarin, kuma ga abin da suke cewa:

 

Karin albashi ba shi ne mafita ba – Aminu Maisalati

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

“A gaskiya karin albashin da ake yi wa ma’aikata daga lokaci zuwa lokaci ba shi ne mafita ga ma’aikatan da kuma tattalin arzikin kasar nan ba.  Idan aka lura, shekaru nawa aka yi ana kara albashi amma har yanzu babu wani canji? Mafita ita ce gwamnati ta gyara tattalin arzikin kasa, ta samar da komai cikin sauki, ta saukaka wa ’yan kasuwa wajen gudanar da harkokin kasuwanci, a samar da masana’antu da inganta bangaren samar da  wutar lantarki da man fetur da sauran muhimman bangarori, sai ka ga dan albashin da ake ba ma’aikaci ya ishe shi rayuwa daidai gwargwado.

ADVERTISEMENT

Amma da zarar an kara albashi, to su ma ’yan kasuwa za su kara farashin kayayyaki ne, inda hakan zai shafi kowane dan kasa, ba ma’aikaci kadai ba.”

 

Na goyi bayan a rika kara wa ma’aikata albashi – Hannatu Labaran Ali

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

“A ra’ayina game da batun a rika kara wa ma’aikata albashi, hakan ya yi daidai.  Hasali ma hakan zai rika karfafa wa ma’aikata gwiwa wajen ci gaba da nuna kwazo a wajen gudanar da aiki ba tare da nuna kasala ba.  Sannan idan aka kara wa ma’aikaci albashi, yana rage matsalar karbar cin hanci da rashawa da ita ce babbar matsalar kasar nan.  Sannan ’yan kasuwa ma za su shaida ganin yadda ma’aikata za su rika tururuwa zuwa kasuwa don yin sayayya. Don haka karin albashi ga ma’aikaci yana da matukar fa’ida.”

 

Karin ya yi daidai – Alhaji Abdullahi Ibrahim

Musa Kutama, Kalaba

“Gaskiya karin albashin ma’aikata da Shugaban Kasa muhammadu Buhari ya yi ya dace, kuma ya yi a kan lokacin da ya dace. Don haka abin a yaba ne domin karin zai rage radadin karancinsa musamman ga masu iyali.”

 

Karin albashi ya dace sai dai…. – Alhaji Umar Farouk

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

“A zahirin gaskiya karin albashi abu ne da ya dace idan aka yi la’akari da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a yanzu kuma idan ka duba galibin ma’aikata suna zaune ne a gidajen haya musamman kananan ma’aikata. Idan ka duba shari’o’in da suka shafi bashi da gidan haya a yawancin kotunan Najeriya za ka tarar kananan ma’aikata ne suka fi yawa kafin kananan ’yan kasuwa. Sai dai matsalar da ake gudu kawai ita ce sake tashin farashin kayayyaki daga ’yan kasuwa musamman idan sun ga karin albashin ya fara aiki amma idan ba haka ko ma dai mene ne, karin albashin yana da kyau.”

 

Karin albashi ya dace – Ado Lawal

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

“Ra’ayina shi ne karin albashi da gwamnati ta yi ya dace koda dai ba shi zai magance musu dukkan bukatocinsu ba. Tun farko ma bai kamata ya zama wani abu da sai an yi ta kai ruwa rana ba kafin a cimma nasara amma da yake kasar ta gaji haka sai a dauka wata bajinta ce. Bayan haka bisa la’akari da al’adar kasar nan duk lokacin da aka samu karin albashi to a saurari hauhawar farashin kayayyaki kuma tunda babu wani kayyadajjen farashinsu a kasuwa wannan shi ma wani tarnaki ne da yake zuwa da karin albashi alhali mafi yawan ’yan Najeriya ba ma’aikata ba ne sai dai kuma a kansu karin albashi ke karewa.”

 

Dama can albashin ya yi karanci – Alhaji Habibu Sule

Musa Kutama, Kalaba

“Karin albashi da Shugaban Kasa ya yi ya dace domin ai dama albashin ba ya biya wa wadansu cikakkun bukatunsu, amma karin na yanzu zai rage masu wani abu, don haka a nawa ra’ayin wannan karin ya yi daidai ya kuma dace.”

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya