✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Trump ya kaddamar da yakin neman zaben wa’adi na biyu

Yayin da yakin neman zaben Shugaban kasar Amurka na 2020 ke karatowa, Shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da yakin neman zabensa gaban cincirindon magoya…

Yayin da yakin neman zaben Shugaban kasar Amurka na 2020 ke karatowa, Shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da yakin neman zabensa gaban cincirindon magoya bayansa, inda ya tabo wasu batutuwa masu sarkakkiya baya ga shagube da yayi ta yi na burge magoya bayansa.

Mista Trump ya kaddamar da yakin neman zaben ne a wani gangami a birnin Orlando na jihar Florida, daya daga cikin muhimman jihohin da suka taimaka masa yin nasara a zaben shekarar 2016. Inda ya bukaci magoya bayansa su “tabbatar da wannan tafiya” tsawon wasu shekaru hudu masu zuwa.

Shugaba Trump ya koma kan alkawarin yakin neman zabensa na 2016 game da murkushe haramtattun bakin haure, inda yayi gargadin cewa masu kalubalantarsa na jam’iyyar Dimokrat na son halasta wa ‘yan ci-rani tsallaka iyakar kudancin kasar.

Mahalarta gangamin sun yi masa maraba ta hanyar fadin “USA” abin da ya tuna masa da yadda ya fara yakin neman zabe shekaru hudu da suka gabata.

Ya ce “wannan wani sauyi ne da mutane suka fara…. Wadanda suka yi imanin cewa dole sai kasa ta fara kula da ’yan kasarta da farko.”

Shugaba Trump, a jawabin ya kira wasu kafafen yada labaran Amurka da cewa ‘makaryata ne.’

Kwana guda kafin nan, shugaban ya wallafa sakon Tiwita cewa hukumomi za su fara “fitar da miliyoyin bakin haure wadanda suka shiga Amurka ta haramtacciyar hanya.”