✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karon battar jihohi 6: APC da PDP sun sake sa zare

A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ba a kammala zaben gwamnoni a jihohi shida…

A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar Zabe Mai zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ba a kammala zaben gwamnoni a jihohi shida na kasar nan ba, inda ta ce za a gudanar da zaben raba-gardama a ranar Asabar din makon gobe.

Jihohin da za gudanar da zaben raba-gardamar sun hada da Kano da Bauchi da Sakkwato da Filato da Adamawa da Benuwai, inda manyan jam’iyyun kasar nan APC da PDP suka sa zare don nuna kwanjinsu a jihohin.

Bayyana zaben Gwamna a matsayin wanda ba a kammala ba ya janyo musayar yawu a tsakanin jam’iyyun biyu a jihohin biyu, inda APC da PDP suka rika zargin juna da yi wa juna yarfe da kazafi, inda suka sha alwashin kai bantensu a zaben raba-gardamar.

A Kano magoya bayan APC da PDP sun koma ga Allah ta hanyar gudanar da addu’o’i da karatun Alkur’ani don samun nasarar ’yan takararsu. Yayin da wadansu magoya bayan dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf suka yi Alkunuti suna rokon Allah Ya karya wadanda suke ganin sun hana nasarar da suke zargin ya samu a zaben da aka gudanar makon jiya.

Kafin yanke shawarar gudanar da zaben raba-gardamar Hukumar INEC ta bayyana yawan kuri’un da kowace jam’iyya ta samu inda a Jihar Kano Jam’iyyar PDP ke kan gaba da kuri’a miliyan1 da dubu14 da 474, Jam’iyyar APC kuma tana da kuri’a dubu 987 da 819.

Jami’in Tattara Sakamakon Zabe a Jihar Kano Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ya ce hukumar ta dauki wancan mataki ne lura da cewa an soke kuri’a dubu 49 da 761 a wasu wurare saboda wasu dalilai, baya ga mazabar Gama da sakamakonta ya bata saboda hargitsin da wadansu suka tayar lokacin tattara sakamakon zaben Karamar Hukumar Nasarawa, kuma yawan kuri’un ya zarta tazarar da ke tsakanin ’yan takarar jam’iyyun biyu.

Sai dai a yayin da PDP ke zargin an shirya zaben raba-gardamar ne don a dakile nasarar dan takararta Abba Yusuf, Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ya fadi a wata takarda cewa Jam’iyyar APC da dan takarar Gwamnanta na Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje suna sane da duk hanyoyin da Jam’iyyar PDP ta yi amfani da su wajen magudin zabe ta hanyar sayen kuri’u da tsoratar da masu zabe wanda a cewarsa jam’iyyarsu ta APC ta himmatu wajen toshe duk wadannan hanyoyi.

Malam Muhammad Garba ya ce APC ta yi shiri sosai don tunkarar zaben da za a sake yi a ranar 23 ga watan nan inda za ta samu kuri’un da za su girgiza dan takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf  da magoya bayansa. “Jam’iyyar APC tana shiri kuma tana da tabbacin samun nasara a zaben saboda kananan hukumomin da za a sake zaben wurare ne da Jam’iyyar APC ke da karfi kuma dukan masu zabe a wurin sun yanke shawarar sake kada wa Gwamnan kuri’unsu,” inji shi.

Shi ma dan takarar Jam’iyyar PDP, Abba Yusuf ya tabbatar wa magoya bayansa samun nasara a zaben da za a sake a jihar. A wata takarda da Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu Abba  Yusuf ya ce Jam’iyyar PDP tana sane da irin magudin da Jam’iyyar APC ta tafka a zaben da aka gudanar inda ta zurara kuri’u da kuma soke zabubbukan wasu akwatuna lamarin da ya janyo Hukumar INEC, ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Ya ce baya ga haka mutanen Kano sun ga yadda makiya ci gaban dimokuradiyya wadanda manyan jami’an gwamnati ne suka lalata aikin hada sakamakon zaben da nufin hana PDP samun nasara a zaben.

Sanusi Dawakin Tofa ya yi zargin cewa wadansu jami’an gwamnati sun shiga mazabar Gama a Karamar Hukumar Nasarawa suna sayen kuri’a a kan Naira dubu biyar tare da karbar katin zabe daga hannun al’ummar yankin inda a cewarsa ’yan sandan Gwagwarwa  sun kama mutum biyu daga cikinsu. Sai ya yi kira ga magoya bayan PDP su kwantar da hankalinsu domin jam’iyyar ce ke da nasara lura da cewa ita ce take kan gaba a kuri’un da aka kirga a baya.

Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya bukaci al’ummar jihar su zauna lafiya kuma su guji duk wani abu da zai jawo hargitsi ko tashin hankali.

Sarkin ya kuma yi kira ga jama’a su kyale Hukumar INEC ta gudanar da aikinta yadda ya kamata kamar yadda aka dora mata.

A Jihar Bauchi,  Babban Jami’in Tattara Sakamaon Zaben Farfesa Mohammed Kyari, ya ce baya ga soke daukacin sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa saboda aikata rashin gaskiya, za a kuma gudanar da zaben raba-gardama a wasu rumfunan zabe a sassan jihar.

Bayyana zaben Gwamnan Jihar da wanda bai kammala ba, ya sanya jam’iyyun APC da PDP a Jihar sake sanya zare don fafatawa a zaben na mako mai zuwa.

Sai dai a yayin da jam’iyyun biyu ke kokarin lashe zaben raba-gardamar, dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar  PDM, Alhaji Ahmed Iliyasu ya yi zargin cewa an cire sunan jam’iyyarsa da shi kansa a cikin jerin ’yan takarar Gwamnan Jihar don haka zai je kotu.

Farfesa Mohammed Kyari ya ce a zaben da aka gudanar a kananan hukumomi 19 daga cikin 20 Jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri’a dubu 469 da 512 sai APC ke bin ta da kuri’a dubu 465 da 453, sai PRPmai dubu 45 da 735.

Soke zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa ya biyo bayan rahoton da Jami’ar Tattara Sakamakon Zaben a yankin, Misis Dominion Anosike ta bayar cewa an tilasta mata ta sanar da sakamakon zabe a karamar hukumar ta hanyar barazana ga rayuwarta kuma an far mata saboda haka sakamakon zaben da ta zo da shi ba a kan takardar da ake rubuta sakamakon zaben aka rubuta shi ba. Kuma ta ce an tilasta mata shigar da abubuwan da ba su dace ba a lokacin tattara sakamakon zaben.

Wakilin Jam’iyyar APC a wajen tattara sakamakon zaben, Kanar Umar Tilde (mai ritaya) ya bayyana sakamakon zaben da na bogi wanda aka tsara a gefe, don haka ne ya bukaci a yi watsi da shi. Kanar Umar Tilde ya ce, “Sakamakon zaben ya sha bamban da wanda wakilan jam’iyyarmu suka bayyana mana. An yi barazana ga jami’an gudanar da zaben da kuma tilasta musu bayyana sakamakon zabe a yanayin da bai dace ba.”.

Nan take aka yi watsi da sakamakon zaben, inda aka ce za a gudanar zaben raba-gardama a ranar da hukumar ta ajiye.

A wani taron manema labarai Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi Alhaji Uba Ahmad Nana ya ce matakin da Hukumar INEC ta dauka ya yi daidai, inda ya zargi PDP da haifar da dukan matsalolin da aka samu a zaben amma tana neman boye kuskurenta, “Wannan wani abu ne da ya zama halin ’ya’yan PDP, su yi laifi su nemi dora wa wani laifin, dukan zarge-zargen da suke yi mana laifinsu ne.

Ya ce an tilasta Baturiyar zabe bayyana sakamakon da ba shi ne ba da kuma yi mata barazana kamar yadda ta bayyana da kanta. Don haka an rubuta ne an bai wa PDP nasara, ba mutanen APC ne suka tilasta wa jami’ar zaben ba, dole ne ya zama dan PDP ne” inji shi.

Ya ce Jam’iyyar APC, jam’iyya ce mai bin doka, kuma da yardar Allah idan an sake zaben suna hangen nasara.  Sai Alhaji Uba ya yi kira ga magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da addu’a sukuma jira ranar sake gudanar da zaben, su fito su zabi Jam’iyyar APC

Ita kuwa Jam’iyyar PDP ta yi tir da matakin da Hukumar INEC ta dauka na soke zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya bukaci Gwamnan Jihar, Mohammed Abubakar ya mika ragamar mulkin jihar ga gwamnati mai shigowa tunda al’ummar jihar sun ki sake zabensa a zaben da aka gudanar ranar Asabar din makon jiya.

Dogara ya ce soke zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa da Farfesa Mohammed Kyari ya yi haramtacce ne kuma danniya ga al’ummar jihar.

Ya yi kira ga Shugaban Hukumar INEC ta Kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu ya kawo dauki a kan rikicin da ke fuskantar jihar, ya ce sanar da rashin kammala zaben kamar fashi da makami ne aka yi wa al’ummar Jihar Bauchi.

Dogara ya ce wadanda suka kai farmaki wajen tattara sakamakon zaben an san su kuma motar da suka yi amfani da ita an san ta, an san mai motar kuma sojoji sun kama mutum uku daga cikinsu da motar duk an mika ga ’yan sanda.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi Alhaji Hamza Koshe Akuyam ya ce wadanda suka ta da rikicin sun yi ne bayan sun tabbatar da cewa PDP ce ke yin nasara.

Ya ce jam’iyyar tana rokon a sauya Kwamishinan Zabe da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi domin sun yi katsalanda a cikin harkokin siyasa.

Shi kuwa dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Ja’miyyar PDM, Alhaji Ahmed Iliyasu ya zargi Hukumar INEC ne da cire sunan jam’iyyarsa daga cikin jam’iyyun da suka yi takarar Gwamnan jihar bayan sun cika dukan ka’idojin shiga takarar.

Alhaji Iliyasu ya ce cire alamar jami’yyarsu ya jefa magoya bayansu cikin dimauta da rashin sanin inda za su dosa a lokacin zaben da aka yi, don haka zai kalubalanci Hukumar INEC a gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zabe.

Dan takarar Jam’iyyar PDP Sanata Bala Mohammed da Gwamnan Jihar Mohammed Abdullahi Abubakar na APC za su yi fafatawar karshe don samun kuri’a mafi rinjaye a Karamar Hukumar Tafawa Balewa da sauran rumfunan zabe a kananan hukumomi 15 da jihar da suke dauke da kuri’a dubu 184 da 552.

A Jihar Sakkwato zaben Gwamnan na ranar Asabar ya bai wa jama’a da dama mamaki, ganin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal wanda jam’iyyarsa ta PDP ta sha  kaye a zaben Shugaban Kasa da Majalisar Dokoki ta Kasa ya bai wa dan takarar Jam’iyyar APC Alhaji Ahmad Aliyu rata a zaben.

Bayan soke sakamakon rumfunan zabe 136 da suke dauke da masu jefa kuri’a dubu 75 da 403, Jam’iyyar APC ta hada kuri’a dubu 486 da 145, yayin da PDP ke da dubu 489 da 558 wato akwai bambanci kuri’a dubu 3 da 413 a tsakaninsu.

Baturiyar zaben Farfesa Fatima Bature Mukhtar, ta bayyana sakamakon zaben a matsayin wanda bai kammala ba, saboda kuri’un da aka soke sun fi tazarar da Tambuwal (PDP) ya bai wa Ahmadu (APC).

Tuni Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi watsi da wannan mataki, inda ya bukaci hukumar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ba tare da yin zaben raba-gardama ba. Gwamnan ya yi barazanar zuwa kotu kan abin da ya kira neman hakkin Sakkwatawa da suka zabe shi.

Ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya kira a Sakkwato a ranar Litinin da ta gabata, ya ce ba wata doka da ta samar da zabe bai kammala ba a kundin tsarin mulki bayan akwai mai rinjaye.

“Ba wannan tsarin a kundin mulkin kasar nan, don haka za mu tafi kotu don a warware mana,” inji shi. Gwamnan ya nemi hukumar zabe ta sake duba hukuncinta saboda a cikin kundin tsarin mulki maganar wanda ya samu nasara ya yi a sashe na 179 (2).

“Ba za mu bar kowane mutum ya lalata zabin jama’a ba. Kowane jami’in hukumar zabe yana da sunan da yake karewa,” inji shi.

To amma Gwamnan ya nemi magoya bayansa su zamo masu bin doka da oda kuma su fito kwansu da kwarkwata su zabi PDP a zaben da za a sake duk da za su tafi kotu.

Dan takarar Jam’iyyar APC Alhaji Ahmad Aliyu ya ce shi da jam’iyarsa sun karbi hukuncin Hukumar INEC da zuciya daya. Ya ce wuraren da za a sake zaben jam’iyyarsu ke da rinjaye sosai kamar Karamar Hukumar Gada da Kebbe da Goronyo don haka ya ce jam’iyyarsu za ta samu nasara da tazara mai yawa.

Ya zargi jam’iyya mai mulki da cin zarafin magoya bayansu da amfani da jami’an tsaro na bogi ana kai musu farmaki da tunzurawa.

Ya ce abin da magoya bayan PDP ke fada cewa da su ke da rinjaye hukumar zabe ba za ta bayyana zaben bai kammala ba, ba gaskiya ba ne. Ya tuna musu cewa a zaben dan Majalisar Wakilai  na Tureta/Dange Shuni/Bodinga, dan APC ne a gaba amma aka bayyana zaben bai kammala ba duk da ya bai wa dan PDP ratar kuri’a 3,000 kuma kuri’a 4,000 da aka soke. “Me ya sa ba su yi korafi ba? Hukuncin da jami’ar zaben ta yanke yana cikin dokar zabe ta 2010 da aka yi wa gyaran fuska,” inji shi.

Ya ce sun bukaci magoya bayansu kan su fadakar da mutane amfanin zabar jam’iyyarsu a zaben da za a sake a kananan hukumomi 22 na jihar.

Kwamishinan Zabe na Jihar Sakkwato Alhaji Sadik Musa ya ce hukuncin da suka yanke yana cikin tsarin doka. “Zaben za a sake ne a rumfunan zabe 136 da aka soke saboda hargitsi da saba wa dokokin zabe da cin zarafin ma’aikatanmu. An zo fadin sakamako kuma ratar ba ta fi yawan kuri’un da muka soke ba, za a sake don sakamakon na iya canjawa,” inji shi.

A Jihar Filato ma Baturen Zaben Farfesa Richard Kimbir ya ce tazarar da ke tsakanin dan takarar Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Simon Lalong ya ba dan takarar Jam’iyyar PDP Jaremiah Useni ita ce ta kuri’a dubu 44 da 929, kasa da kuri’a dubu 49 da 377 da aka soke lokacin zaben. Ya ce Simon Lalong na APC ya samu kuri’a dubu 583 da 255, yayin da Jerry Useni na PDP ya samu kuri’a dubu 538 da 326, don haka za a sake fafatawa a zaben raba-gardama don fitar da zakara.

Gwamnan Lalong ya bukaci al’ummar jihar su kwantar da hankalinsu game da wannan mataki da Hukumar INEC ta dauka, inda ya bukaci mutanen mazabun da aka soke zabensu su fito su kada kuri’a a ranar zaben tare da zabar jam’iyyarsa ta APC.

A Jihar Adamawa inda dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya fito, Babban Mai tattara Sakamakon Zabe na Jihar, Farfesa Andrew Haruna ya ce Jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri’a dubu 367 da 471, yayin da APC ke da kuri’a dubu 334 da 995, inda ake da tazarar kuri’a dubu 32 da 476, alhali an soke kuri’a dubu 40 da 988, don haka ya bayyana cewa zaben bai kammala ba.

Kwamishinar Zabe ta Jihar, Farfesa Fatima Muktar ta Jihar ta bayyana cewa zaben bai kammala ba ne saboda tashe-tashen hankula da aka samu a wasu mazabu a sassan jihar, inda ta bukaci ma’aikatan da ke aikin zabe a yankunan da ake rikici su kai rahoto ga Hukumar INEC a jihar.

Hukumar ta yi da’awar cewa a wasu wurare an yi garkuwa da ma’aikatanta sannan an lalata kayayyakin aiki da takardun sakamakon zaben.

A Jihar Benuwai an shata daga ce a tsakanin Gwamna Samuel Ortum na Jam’iyyar PDP wanda ke gaba da kuri’a dubu 410 da 576 da Emmanuel Jime na APC mai kuri’a dubu 329 da 22. Babban Mai Tattara Sakamakonn Zaben Jihar, Sebastian Maimako ya ce zaben bai kammala ba ne, saboda an lura akwai dimbin masu jefa kuri’a da ba su iya yin zaben ba, saboda ba a gudanar da zaben a yankunansu ba.