✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karuwa ta sace motar ubangida a hannun direba

Wani direba mai suna bictor Dissa ya shiga tsaka-mai- wuya bayan da wata karuwa da ya dauka ta yi awon gaba da motar maigidansa kirar…

Wani direba mai suna bictor Dissa ya shiga tsaka-mai- wuya bayan da wata karuwa da ya dauka ta yi awon gaba da motar maigidansa kirar Kia, wacce aka kiyasta kudinta a kan Naira miliyan 4 da rabi.

Direban mai kimanin shekara 54 yana aiki da wani kamfani ne da ke Ikoyi a Jihar Legas, inda yake tuka maigidan nasa, ya kuma kasance yana tafiya da motar gidansa, sannan da safe ya tuko ta ya dauki maigidansa ya kai shi ofis.

Aminiya ta jiyo cewa, a ranar da lamarin zai auku, bayan ya sauke maigidan nasa sai ya je Unguwar Obalende, inda ya dauki karuwar wacce ya ce ya san ta ne kimanin mako guda bayan ya kai ta gidansa suka gama abin da suke sai ya ba ta motar ta tuko su suka fito waje.

Daga nan sai ta bukaci su kara mai a motar, shi ya sauka daga motar domin ya ga yadda za a zuba man a gidan mai da ke kan titin Awolowo a Ikoyi. Saukarsa daga motar ke nan, sai ta dage gilashi ta bai wa motar wuta, ta tafi da ita. Daga nan ya shigar da maganar sace motar a ofishin ’yan sanda a yankin.

Jami’in dan sandan da ya gabatar da direban a gaban Kotun Majestari, Saje Faransis Job ya tuhumi wanda ake zargin da laifin kage da shirya sata, wanda ya ce ya saba wa sashi na 411 na kundin dokar laifuffuka na Jihar Legas na shekarar 2015.

bictor Dissa dan asalin kasar Benin ya musanta aikata laifin, inda Majestare Y.O. Aro-Lambo ya ba da belinsa a kan Naira miliyan daya da kuma mutum biyu da za su tsaya masa, kowannensu a kan Naira miliyan daya, ya kuma dage sauraron karar zuwa gaba.