✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasashen Girka da Turkiyya na neman gyara dangankatarsu

Shugabannin kasashe biyu na Kungiyar NATO, wato Girka da Turkiyya, sun gana a birnin Ankara a wani yunkuri na inganta dangantakarsu. Akwai tarin matsaloli a…

Shugabannin kasashe biyu na Kungiyar NATO, wato Girka da Turkiyya, sun gana a birnin Ankara a wani yunkuri na inganta dangantakarsu.

Akwai tarin matsaloli a tsakanin kasashen biyu da suka hada da rikicin iyaka da batun dadadden rikicin Tsibirin Cyprus wanda ya ki ci, ya ki cinyewa.

Shugaban Turkiyya Receb Tayyip Erdogan da bakonsa Firayi Ministan Girka Aledis Tsipras sun gana cikin annashuwa, a ganawar da suka yi da maneman labarai, amma ba su bata lokaci ba wajen bayyana bambancin da ke tsakaninsu.

Babban batun da ya fi damun Shugaba Erdogan shi ne na juyin mulkin da ba a yi nasara ba na watan Yulin 2016.

Ya bukaci Girka ta mayar da mutanen da ya kira maciya amanar kasa, wadanda suka hada da sojojin Turkiyya takwas da suka tsere zuwa Girka a cikin wani jirgi mai saukar ungulu.

A watan Mayun bara ne Kotun Kolin Girka ta amince a bai wa daya daga cikinsu mafakar siyasa, matakin da ya fusata Turkiyya.

Daya batun kuma shi ne makomar Tsibirin Cyprus. An dai raba wannan tsibiri gida biyu ne – inda Girkawa ke da rinjaye – tun bayan da Turkiyya ta auka wa Tsibirin a 1974 a matsayin wani martani ga wani yunkurin juyin mulki da Girka ta mara wa baya.

Shugaba Erdogan ya ce mutanen Turkiyya mazauna Tsibirin Cyprus na da muhimmanci a wurinsa sosai- wanda ke nufin zai nemi a ba su damar amfana da albarkatun mai da aka samu a tsibirin kamar yadda BBC ya ruwaito.

Batu na gaba shi ne na gudun hijira. Turkiyya ba ta gamsu da kudaden da aka alkawarta mata ba na daukar nauyin ’yan gudun hjira daga wasu tsibirai na Girka a karkashin wata yarjejeniya da ta sanya wa hannu da Tarayyar Turai kusan shekara uku da ta gabata.

Amma akwai wani batun daya da ya faranta wa Turkiyya rai, shi ne cewa Girka na goyon bayan a shigar da Turkiyya cikin Tarayyar Turai – matakin da yawancin kasashen Turai suka dade da yin watsi da shi.