✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 90 na kifin da ake ci a Abuja daga Kudu maso Yamma ne – Isa Zariya

Aminiya: Sai ka fara da gabatar da kanka. Sunana Alhaji Isa Abdullahi Zariya, ni shugaba ne na kungiyoyin masu harkar sayar da kifi na al’ummar…

Aminiya: Sai ka fara da gabatar da kanka.

Sunana Alhaji Isa Abdullahi Zariya, ni shugaba ne na kungiyoyin masu harkar sayar da kifi na al’ummar Arewa a nan Abuja. Mun kafa kungiyar kamar shekara biyu da su ka wuce bayan kula da yadda wasu da su ka shigo harkar daga baya a nan yankin Abuja ke neman kwace sana’ar daga wajenmu mu kuma mu koma ’yan kallo.

Aminiya: Yaushe ka fara harkar sayar da kifi?

Na fara wannan harka kamar shekara 20 a nan Abuja a lokacin Marigayi Shugaban kasa, Janar Sani Abacha, sai dai idan ana maganar kama kifin ne to anan gadonsa na yi, saboda iyayena shi su ka sani. To a lokacin tsohon shugaban kasa Obasanjo ne ministan Abuja malam Nasiru El-rufai ya dawo da mu wajen nan na Kasuwar kifi ta Kado, ya bamu rumfunan sayar da kifi da kuma fili wanda mu ne mu ka gina shagunan don ajiyan kifi. An bada Kasuwar tun a lokacin ministan Abuja Jeremiah Useni a karkashin wani darakta na Agric mai suna Dokta dan Baba. 

Sai dai a maimakon a raba filin kai-tsaye ga ma’abota harkar, sai a ka raba su ga jami’an gwamnati, dan kadan ne da a ka ware a ka nemi jama’armu su yi kuri’a a kai, inda cikin mutum kamar 100 da su ka biya dubu goma-goma, bai fi mutum uku ba ne su ka yi nasara a yayin kur’ar, ragowar kuma su ka yi asara. Haka kasuwar ta yi ta zama ba jama’a a cikinta. To zuwan Malam Nasiru El-rufai ne bayan ya gano cewa akwai ginanniyar kasuwa ta masu kifi amma ga sunan suna warwatse, sai wasu da su ka san abinda ya faru su ka tsegunta masa, shi kuma ya gayyacemu ya ce mu je mu yi kungiya zai raba mana rumfuna da shaguna a wajen. 

To bayan kamar wata bakwai ana kai kawo zuwa wajen minista tare da wasu jagorori da na shugabanta, sai minista ya tattaro gaba dayan masu sana’ar ya kawo mu nan aka raba mana rumfuna, sannan ya soke ikon mallakan fili na wadanda su ka gaza gina shaguna ya bamu. 

Wadanda su ka yi nisa a aiki kuma aka bar su su ka karasa, mu ma mu ka gina namu, sannan ya zo ya bude kasuwar da kansa kuma tun daga lokacin ta yi ta bunkasa har ta kai matakin da ta ke kai a yau. Wannan alheri da ya yi mana ba za mu taba mancewa da shi ba. Akwai shagunan sayar da abincin kifi da magungunansu, inda ake zuwa daga jihohin nesa da na kusa ana saya, akwai kuma bangaren masu nama da makamantansu da aka shigo da su daga baya don kara raya kasuwar kasancewar kifi kadai ba zai cika kasuwar ba.

Aminiya: Kamar wadanne irin nau’ukan kifi ku ke samarwa a nan?  

A jimlace da ma kifi ya kasu zuwa nau’i uku. Akwai wanda mu ke kira kifin ruwa wanda a ka kama a rafukan kasar nan, akwai na kiwo da a ke kawo su da ransu, sai kuma daskararren kifi da ake kawowa daga ketare. Shi na ruwa da ya hada da giwar ruwa wato “Croaker” an fi kawo su ne daga yankin Shiroro a Jihar Neja da Jihar Kogi da Tiga dam na Kano da Makurdi da Adamawa da Taraba da tabkin Chadi a Jihar Borno. 

Su kuma kifi na kiwo wanda yawanci tarwada ne kusan duk daga jhohin kudu maso yamma ne a ke kawo mana su nan wato yankunan yarabawa. Kusan kashi 90 a cikin 100 na kifin da ake ci anan Abuja daga yankunan yarabawa ne ake kawo su, kamar ragowar kashi 10 ne kawai wanda aka yi kiwonsu a nan Abuja da ragowar yankunan jihohin Arewa na kusa da Abuja. Hakan kuma ya faru ne a sakamakon irin tallafin da su ka samu a lokacin tsohon shugaban kasa Obasanjo wanda ya ba su fifiko. 

Shi kuma daskararren kifi ana kawo su ne daga kasashe irin Chana da Ajantina da sauran kasashe na Latin-Amurka a cikin katan-katan sunanan makare a dakunan sanyi na kasuwar nan kuma sun ma fi saukin farashi fiye da kifin da ake samu na gida.

Aminiya: Zuwan Gwamnatin Buhari ta haramta shigo da kifin waje, ya aka yi ake samunsa a kasuwar nan?

Wannan haka ne. An sa dokar ne bayan hukumar NAFDAC ta koka a kan irin sinadaran magungunan ajiya da ake sawa kifin na waje wanda ta ce ya na iya yin lahani ga mai amfani da shi. Sai dai kamar yadda kasan lamarin kasar nan har yanzu ana kawo su ta barauniyar hanya, sai dai duk da cewa sun fi sauki, jama’a sun fi sayan na gida wanda a kullum ana sauke kamar na miliyan 20 zuwa 30 a kasuwar nan. 

Aminiya: Wace irin nasara za ka ce kun samu tun lokacin da aka dunkule ku a waje guda?

Nasarorin su na da yawa. Na farko dai shi ne samun wannan waje da kullum darajarsa karuwa ya ke yi. A Wannan rumfa tawa da ka gani mu wajen goma ne a cikinta kowa ya ke cin abinci daga matsuguninsa. 

A lokacin da kasuwar ta fara, rumfa guda ba ta wuce naira dubu dari da hamsin ba idan ta yi tsada ne naira dubu dari biyu. Amma a yau kudin rumfa guda ya kai naira miliyan uku zuwa hudu. Kuma baya ga wannan bangare da ka ganmu a ciki, akwai wasu bangarori daban da suka hada da na masu kifin banda, sai kuma na masu sayar da nama, gaba daya adadin rumfunan za su kai 30. Wannan ba karamin ci gaba ba ne. To gashi yanzu har ta kai jihohi makota anan su ke zuwa su sayi abincin kifi da wasu ’yan kasuwar nan ke kawowa kai-tsaye daga bakin ruwa su sauke.

Aminya: Ya batun matsala kuma?

Babbar matsalar da ta fi damunmu ita ce ta karancin wutar lantarki wanda sai da shi ne injunan da ke dakunan ajiyan kifi na sanyi za su yi aiki. Kifi da aka kama a rafuka wanda ake kira fresh fish da kuma na waje duk suna bukatar ajiya. To idan ba wutar nan dole sai mun yi amfani da inji don gudun kar su lalalace, sai dai Alhamdu Liillahi yanzu mu na samun wuta bakin gwargwado.

Aminya: A karshe wane irin karin tallafi ku ke bukata daga gwamnati don bunkasa wannar harka

Mu na bukatan gwamnati ta taimaka mana ta fuskar tallafin kayan gudanar da wannan harka da kuma horo da karin jari don bunkasa kiwon kifi ba sayarwa kawai ba, tare kuma da inganta abincin kifi da wasu daga cikinmu su ka fara don rage shigo da na waje kamar yadda yankin kudu maso yamma su ka samu a baya. 

Sannan kuma a kara bude hanyar shigo da bushashshen kifi dake zuwa daga bangaren Baga na jihar Borno. Mun san irin kokarin da shugaban sojojoji Janar Tukur Yusuf Burutai ya yi a wannan fuska na dawo da lodin tirela kamar sau biyu a mako daga yankin wanda hakan ya sa farashin kifi ya karye daga naira dubu 50 a kan kowane katan zuwa dubu 37 a nan Abuja. Sai dai har yanzu mu na kira da a kara yin sassauci akan lamarin tun daga wurin kamun kifi har zuwa yin lodinsa wanda a baya ake yi a kullum.