✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katsinawa da Daurawa mazauna Legas sun yi addu’ar zaman lafiya ga jihohin Arewa

Al’ummar Katsinawa da Daurawa mazauna Jihar Legas sun shiryar addu’a ta musamman ga wasu daga cikin jihohin Arewa da ke fama da matsalolin tsaro da…

Al’ummar Katsinawa da Daurawa mazauna Jihar Legas sun shiryar addu’a ta musamman ga wasu daga cikin jihohin Arewa da ke fama da matsalolin tsaro da kasa baki daya.

Kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Legas wacce Alhaji Abubakar Sanusi Faskari Danburan na Katsina ke jagoranta ne ta shirya taron addu’ar a harabar ofishin Jihar Katsina da ke Legas a karshen makon jiya, inda aka gudanar da saukar Alkur’ani Mai girma tare da addu’ar samun dawammamen zaman lafiya a Jihar Katsina da sauran jihohin Arewa da ke fama da matsalar masu garkuwa da jama’a da barayin shanu da ’yan bindiga da ke kisan al’umma. Baya ga addu’ar an jima ana gabatar da jawabai da mukalli inda aka nusar da mahalarta taron hanyoyin da za su bi domin taimaka wa gwamnatin Jihar Katsina da Gwamnatin Tarayya a yunkurinsu na samar da tsaron rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Alhaji Abubakar Sanusi Faskari Danburan na Katsina, wanda ya jagoranci taron ya shaida wa Aminiya cewa, sun taru ne suka shirya addu’a na fatan Allah Ya kawo karshen tada zaune-tsaye da ake fama da su a wasu jihohin Arewa, “Ko a baya kafin a yi zabe mun shirya irin wannan addu’a inda muka nemi taimakon Allah kuma cikin ikonSa an yi zabe an gama lafiya, yanzu kuma mun taru domin neman taimakonSa wajen magance matsalolin tsaro da muke fama da su musamman a Arewacin kasar  nan, domin Shi Allah Mai amsa rokon bayinSa ne,“ inji shi.

Ya ce, Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, yana yin iya bakin kokarinsa don magançe matsalolin don haka ya yi kira ga al’ummar jihar su ci gaba da ba shi hadin kai, “Idan aka lura Mai girma Gwamna Masari shi ne farkon wanda ya fara bullo da tsarin sasantawa tare da tattaunawa domin yin sulhu da masu tada zaune-tsaye, koda yake a wancan lokacin shirin ya gamu da cikas, ni a ganina tsarin tattaunawa tare da tuntubar juna zai yi matukar tasiri wajen magance matsalar. Don haka yunkurin da sabon Gwamnan Jihar Zamfara ya yi abin a yaba ne kuma a sanina koyi ya yi da Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina,” inji shi.

Haka zalika matar marigayi Alhaji Shehu Musa ’Yar’aduwa Hajiya Asabe Musa ’Yar’aduwa, wacce ta albarkaci taron ta shaida wa Aminiya cewa, Allah Yana karbar addu’ar bayinSa don haka suka taru domin yin addu’ar a jam’i baya ga wadda suka saba yi a daidaikunsu. Ta ce akwai bukatar shugabannin Arewa su tashi tsaye su tabbatar sun magance matsalolin da suke addabar yankin.

Asabe ’Yar’aduwa ta ce duk lokacin da ake fama da rikice-rikice, mata da yara kanana ne suka fi shan wuya don haka ta yi kira ga iyaye su kula da bai wa ’ya’yansu tarbiyya domin su zamo na ari abin alfahrin al’umma.