✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kifin da ya fi tsada a duniya ya kai Naira miliyan 653

Wani kifi a kasar Japan mai launin ja da fari da ake kira Koi Carp ya kasance kifin da ya fi kowane rayayyen kifi  da…

Wani kifi a kasar Japan mai launin ja da fari da ake kira Koi Carp ya kasance kifin da ya fi kowane rayayyen kifi  da ake sayarwa daraja inda farashinsa ya kai Dalar Amurka miliyan 1.8 (kimanin Naira miliyan 653), fiye da yadda aka sayar da irinsa a Dalar Amurka miliyan 1.3 (kimanin Naira miliyan 471).

Kifin Koi Carp mai tsawon inci 101 na daga cikin jinsin kifin da ake kira Kohaku wanda wani mai kiwo ya kawo daga gonar kifin Saki a garin Hiroshima babban birnin Japan. Akwai wata da taba samun lambar yabo bayan ta kama irin wannan kifi bara a wani taron nuna bajinta da aka shirya a Japan kuma tana sa ran sake lashe wata lambar yabon a bana saboda magoya bayan da take da su.

Masu sha’awa da masuntan kifin Koi carp suna sa ran bazama a fadin duniya don nemo irin wannan kifin mai daraja da ake saya da tsada.

Wannan dai farashin da aka sayi kifin Koi Carp ya shiga kundin tarihi. Wani masanin halittar kifin Koi dan kasar Birtaniya Tim Waddington, ya bayyana jaridar Daily Mail cewa, samun irin wannan jinsin kifi na Koi mai tsawon inci 101 a cikin nau’in Kohaku ba abin mamaki ba ne.

Jama’a da dama sun yi ta mamakin yadda za a sayar da kifi guda mai irin wannan tsada.

A shekarun baya an samu wanda ya taba samun kyautar Dalar Amurka dubu 500 (kimanin Naira miliyan 182, da dubu 250) saboda bajintar da ya yi na kamo irin wannan jinsin kifi.