✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan gilla: Majalisa ta baiwa Buhari sa’o’i 48 don yin bayani

Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta baiwa Shugaba Muhammadu Buhari  sa’o’i 48 don yi wa ‘yan Najeriya bayani game da shirin Gwamnati da ta ke yi…

Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta baiwa Shugaba Muhammadu Buhari  sa’o’i 48 don yi wa ‘yan Najeriya bayani game da shirin Gwamnati da ta ke yi wajen dakile kisan gillar jama’a da ake yi da hukunta wadanda aka kama da laifi a kasar.

`Yan majalisar sun bukaci fadar shugaban kasa, Ministan tsaro, hafsoshin tsaro da Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya da dai sauran masu fada aji, akan bullo da hanyar magance yawan kisan- gillar da ‘yan bindiga da barayi ke yi a kasar ke yi tare da hukunta su.