✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Khashoggi: Jamus ta dakatar da sayar wa Saudiyya makamai

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa daga yanzu har zuwa lokacin da za a bayar da cikakken haske game da mutuwar dan jarida…

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa daga yanzu har zuwa lokacin da za a bayar da cikakken haske game da mutuwar dan jarida Jamal Kashoggi, kasar ta daina fitar da makamai zuwa Saudiyya.

Merkel ta bayyana hakan ne a lokacin da ta je garin Ortenberg don yakin neman zabe, inda ta tabo batun kashe dan jaridar Saudiyya Jamal Kashoggi inda ta ce “Ku kalli abin da ya faru a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul, wane irin shiririta ce wannan? Ina son na bayyana muku cewar ya zama dole a yi karin haske kan wannan batu. Kuma har zuwa lokacin da za a yi hakan, ba za a sake fitar da makamai zuwa Saudiya ba.”

Saudiyya ita ce kasa ta 2 bayan Aljeriya da ke sayen makamai daga hannun Jamus kamar yadda kafar TRT ta bayyana.

A wata 9 na farkon wannan shekara, Jamus ta sayar wa Saudiyya makamai na kusan Yuro miliyan 417.

A ranar 2 ga watan Oktoba ne Kashoggi ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul a Turkiyya inda bayan shigarsa aka neme shi sama da kasa aka rasa.

Tuni dai Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Adil Al-Zubayr ya bayyana cewa Yariman kasarsu Muhammad bin Salman ba shi da masaniya game da kashe dan jarida Jamal Kashoggi a ofishin jakadancinsu da ke birnin Istanbul na Turkiyya kamar yadda wasu suke zargi.

A sanarwar da Ministan ya yi ga tashar talabijin ta Fod da ke Amurka ya ce Yarima Mai Jiran Gado Muhammad bin Salman ba shi da alhakin kashe Kashoggi saboda bai ma san za a yi hakan ba.

Da a aka tambayi Ministan kan ya za a ce Yariman ba shi da masaniya, sai ya bayar da amsa da cewa, mutanen da ke da hannu a kisan Kashoggi da aka ce suna da alaka ko kuma makusantan Yarima Muhammad ne, ba haka ba ne, ba su da kusanci sam da Yariman.

Al-Zubayr ya ci gaba da cewa “Yarima Mai Jiran Gado ya fito ya karyata duk jita-jitar da ake yadawa kuma ba shi da masaniya kan wannan batu. Haka zalika manyan Shugabannin Hukumar Leken Asiri na Saudiyya ba su da masaniya kan kisan na Kashoggi. Wadannan da suka aikata laifin kananan ma’aikatan tsaro ne. Kuma sun aikata laifukan keta haddi. Sun aikata kuskure bisa kashe Kashoggi a ofishin jakadancin kuma suka yi kokarin boye hakan.”

Al-Zubayr ya kuma ce “Ina son mika ta’aziyya ga iyalansa. Ina jin irin radadin da suke ji. Ina ma dai a ce an iya hana afkuwar wannan abu. Amma an riga an tafka babban kuskure. Ina da imanin duk masu hannu a wannan abu za su fuskanci hukunci.”