✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kishi kumallon mata: Labarin Farida (18)

Falon ya samu kimanin minti daya cikakke cikin shiru. Tsawon dan lokacin nan, daga Baba da abokinsa Mamman har zuwa Yaya Asma’u da uwargida Farida…

Falon ya samu kimanin minti daya cikakke cikin shiru. Tsawon dan lokacin nan, daga Baba da abokinsa Mamman har zuwa Yaya Asma’u da uwargida Farida babu wanda ya furta wata kalma, kamar wadanda aka saukar wa kurumta. Daga bisani ne Mamman Tela ya karya lagon al’amarin, inda ya bijiro da batu na gaba.

“Lallai gaskiyar Malam Bahaushe, da ya ce in ka ji gangami da labari. Kamar kuma yadda ya ce, ruwa ba ya tsami banza. Yanzu idan mun lura, duk wannan sabani ya faru ne a sanadiyyar kishi, don haka ina mafita?” Mamman ya fadi haka, yayin da ya kalli fuskar Yaya Asma’u, alamar kamar da ita yake magana kai tsaye.

“Kishi kuma?” Inji Yaya. “Ban gane batun kishi ba, shin daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki? Yaushe aka yi auren da za a kawo batun kishi nan?”

“Haba Yaya!” Mamman ya kuta, tare da buda baki cikin mamaki. Shin ba ki ji abin da uwargida Farida ta fada ba, ko kin manta abin da ta ce ne?”

Dukkansu suka kara yin shiru na takaitaccen lokaci. 

“…hakika batun auren nan shi ne ya haifar mana da matsala. Ni dai ina da tabbacin muddin ya ce yana kan bakansa game da kara auren nan, to babu wata fahimta da za ta ci gaba da gudana a tsakaninmu.” Yaya ta tuno da korafin da Farida ta yi dazu.

“Don haka, tun da dai mun gane matsalar nan, kada mu bata wa kanmu lokaci, mu tattauna ta kawai, sannan mu fitar da maslaha tsakani.” Mamman Tela dai ya kuke da bayani, har sai da ya gamsar da Yaya Asma’u gaskiyar lamari.

Mutum na gaba da ya yi bayani, shi ne Alhaji Baba. Ya bijiro da matsalolinsa ga wannan taro.

“Babu shakka, kamar yadda abokina ya ankarar, babbar matsalarmu ta faro ne a sanadiyyar batun auren da nake shirin yi. Ba tun yanzu ba matsalar nan ta kunno kai.” Baba na magana, a lokaci guda yana daga kai yana fuskantar fuskokinsu.

“Ni kuma har ga Allah, na kuduri aniyar kara aure ne ba don komai ba, ba don wani laifi da Farida ta yi mani ba. Wannan ’yanci ne kuma hakki ne da Allah Ya ba ni. Idan kuwa aka ce za a uzura mani saboda wannan, ni dai kam ba a yi mani adalci ba.”

“To, to ai…” Farida ta yunkuro za ta yi magana, amma sai Yaya ta daga mata hannu, ta dakatar da ita.

“Kamar yadda na ce, tun da mun gano matsalar ita ce batun kara aure, shin ya dace a Musulunce Baba ya kara aure?” Mamman ya feso tambaya amma kafin kowa ya ba shi amsa, sai ya ci gaba da bayani. “Tun da farko dai aure kamar yadda dukkanmu muka sani, ibada ne. Kowace ibada kuma Allah ake tunkara da ita. Haka kuma babu yadda za a yi ibadarka ta samu amsuwa ga Allah sai ka san yadda ake yin ta, sai ka bi ka’idojinta, ka aiwatar da ita bisa ikhlasi sannan za ta amsu.”

Yaya ta nuna gamsuwa da bayaninsu, sai dai ta so ta furta wani abu, amma Mamman ya ba ta hakuri, ya ce ta kara masa lokaci tukunna ya kammala bayaninsa.

“Tun daga farko, Allah (swt) da Ya zo bayani game da aure, ummurni Ya yi da cewa a auri mata daga biyu, uku har zuwa hudu, idan mutum kuma ya san cewa ba zai iya adalci ba, to ya auri daya ko kuma baiwarsa da ya mallaka. Inda gizo ke sakar shi ne batun adalci. Shin abokina, ka shirya yin adalci tsakaninka da masoyiyarka Farida, idan ka yi auren nan na biyu?” Ya fadi haka a yayin da ya fuskanci Baba da tambayarsa kai tsaye. Wani abin mamaki shi ne, nan take sai Farida ta samu kanta cikin murmushi, wanda haka ya sanya ita ma Yaya ta kyalkyace da dariya.

“Madalla da wannan batu,” inji Baba. “Tun da farko dai, ko ita FATA (Farida Ta Musamman) na bayyana mata kudurina. Zan yi aure ne kawai saboda ina da bukatar raya sunnar Manzon Allah (saw). Na farko dai adalcin da ake magana, shin mene ne? Ni dai a fahimtata, shi ne maganar abinci, sutura, muhalli, kula da tarbiyya da kare mutunci ga dukkan matanka ba tare da nuna bambanci ba. Ni kuwa in sha Allah na kuduri aniyar yin haka ga duk wacce zan aura.”

“Ni matsalata ita ce, batun ba na mutum daya ba ne. Idan kai ka shirya yin adalci, ita wadda za ka auro ka san nufinta? Ba lallai ba ne a ce ta shigo gidanka don Allah ba, sai don abin hannunka. Ni mace ce kuma na san abin da matan zamani suke ciki dangane da aure. Sai mace ta gama wahala da miji, da rana tsaka wata ta shigo ta mallake komai, ko ma ta shiga bokaye da matsafa ta raba ka da mijinka da ’ya’yanka. Wannan shi ne babban abin zullumi.” Farida ta samu bakin magana.

“Yauwa kanwata.” Yaya ta yi tsagal ta furta kalami. “Kin san su maza ba za su fahimci kinaya da kissar mata irin haka ba. Wa ya sani ma kila tun yanzu ta fara mallake masa tunani?”

Gaba daya aka bushe da dariya. A kan haka dai aka daidaita al’amura. Alhaji Baba ya dauki alkawarin ba zai nuna bambanci tsakanin matansa ba, ya kuma dauki alkawarin ci gaba da rike uwargidansa da ’ya’yansa bisa adalci daidai gwargwado. Daga nan kuma Mamman Tela ya roki Farida da ta yi hakuri ta goya wa mijinta baya, ta maida al’amarinta ga Allah.

“Na farko dai Allah Ya albarkace ku da ’ya’ya, ke ce uwargida kuma kin tabbata mijinki yana kaunarki. Ga shi dai Allah Ya huwace wa mijinki arziki. Yana da sana’a, yana da mutunci kuma yana da ilimin bautar Allah daidai gwargwado. Idan kika kwantar masa da hankali, kika bi shi sau da kafa, Allah zai taimake ku gaba daya. Ko kuwa ya kika gani, yayarmu?” Ya fadi haka, a lokacin da ya kura wa Yaya idanu.