✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kishi kumallon mata: Labarin Farida (19)

A karo na uku ke nan Saratu tana neman lambar wayar kawarta Binta amma ba ta samu ba. Abin da na’ura ke gaya mata shi…

A karo na uku ke nan Saratu tana neman lambar wayar kawarta Binta amma ba ta samu ba. Abin da na’ura ke gaya mata shi ne, wayar a kashe take. Amma duk da haka ta ki hakura, domin kuwa tana matukar bukatar yin magana da kawar tata, saboda abin da ke damunta. A karo na hudu, ta sake danna maballin da ya kawo mata da lambarta, ta sake dannawa, amma sakon da aka gaya mata bai canja ba. 

“Kash!” Abin da ta fada ke nan cikin damuwa, bayan ta buga wani uban tsaki. “Ai kuwa Binta ba ta rufe wayarta, me ya faru yau? Lallai ne kuwa in gana da ita yau, domin abin da ke ci mani rai, ita kadai ce za ta iya ba ni shawarar da ta dace.”

Saratu ta ci gaba da korafi ita kadai kamar wacce ke shirin zautuwa. Da ta gaji da buga waya ba ta samu biyan bukata ba, sai ta jefar da ita gefe guda, ta fuskanci wani abin na daban.  Ta shiga cikin damuwa ne, kasancewar yau kwana uku ba ta gana da sahibinta, Alhaji Baba ba. Rabon da ta sanya shi a ido, tun ranar da suka halarci bikin ranar haihuwar Binta. Ta buga masa waya ya fi a kirga amma bai dauka ba sai sau daya. Shi ma kafin ya dauka, sai da ta yi nacin bugawa fiye da sau goma. Bayan ya dauka, maganar da suka yi duka ba ta wuce sakan goma ba. “Ki yi hakuri, ina cikin wata damuwa; zan kira ki.” Abin da ya fada ke nan, kafin ya kashe wayarsa.

Tun daga lokacin nan, ba ta sake samun sukuni ba har sai da ta yi ta bincike. Hasali ma, sai da ta yi zarya fiye da kima zuwa shagonsa na Kantin Kwari amma ba ta samu ganinsa ba. A wannan hakilon nata ne ta gano cewa lallai babu lafiya ne a gidansa. Ta samu labari daga majiyarta cewa, shi da matarsa ne suke sa-in-sa, har ma ta yi yaji. Abin da ya kara tada mata da hankali shi ne, labarin da ta jiwo cewa wannan tata-burza, ita ce ta haddasa ta.

Tana zaune sai ta yi zumbur ta tashi, ta nufi dakin mahaifiyarta, inda ta debi ruwa a kofi ta kwankwada. Ta dawo dakinta ta zauna. Tana zama sai ta rarumi wayarta, ta sake lalubo lambar kawarta ta danna maballin kiranta. A wannan karon, kira daya sai ta ji layin a bude. Nan take ta buga doguwar ajiyar zuciya.

“Aloooo, kawalli! Kina neman sakar mani ciwon zuciya.” Abin da ta fada ke nan, lokacin da ta ji muryar Binta.

“Haba dai, me ya yi zafi haka shi ba wuta ba?”

“Wallahi, ni a yadda nake ji, wannan matsalar tawa ai ta fi wutar ma zafi. Ina matukar son ganin ki.”

“Subuhanallahi! Ba dai wani ne ya mutu ba ko?” Binta ta tambaya.

“Babu wanda ya mutu, ke dai idan kina gida, bari in zo yanzu in same ki. Maganar nan ba ta waya ba ce, mai tsawo ce. Matsaloli biyu ne ke ci mani rai kuma ke ce kadai za ki iya ba ni shawarar da ta dace.”

“Ina gida, sai kin zo.”

“Madalla, ga ni nan zuwa.” Saratu ta nisa, sannan ta kashe wayar. Ba ta bata lokaci ba ta shirya ta fita daga gidansu, ta yi wa gidan su Binta tsinke.

 

Sakonnin Fadar FDk

Ya masu bibiyar Dausayin kauna, gogan naku FDk ya dawo da karfinsa kuma ya sadu da dinbin sakonninku. A yayin da nake kara ba ku hakurin juriyar aiko da sakonnin, a wannan makon, ga kadan daga cikinsu. Muna fatan za a ci gaba da bibiyar filin nan domin ci gaba da fantama sahihiyar soyayya da juna domin Allah: