✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko hayakin turare na da illa?

Likita na taba jin ka ce a likitance yin surace ba matsala. To shi ne nake tambaya yin turare fa da wasu mata sukan yi.…

Likita na taba jin ka ce a likitance yin surace ba matsala. To shi ne nake tambaya yin turare fa da wasu mata sukan yi. Akwai wadanda sukan yi hayakin turare domin gyaran jiki.

Daga Bilki Musa, Jahun

 

Amsa: A’a a likitance ba maganar shakar hayaki a cikin hanyoyin gyaran jiki ko magance cututtuka. Hasali ma hayaki a likitance guba ne ba hanyar magani ko gyara ba. Hayaki ko na wane irin turare ne in dai da itace ko gawayi ko wani makamashi aka kunna shi zai iya fitar da gubar carbon monodide wadda ke iya sarke numfashi. Irin wannan guba ce ke sanadiyyar rayukan da za ki ji an ce an rasa sakamakon kwana da injin janareta a gidan da hayakin injin bai samu fita ba, ko a gidan da aka yi gobara, ki ji an yi rashi duk da cewa wuta ba ta taba wanda aka rasa ba. Hayaki ne duka sanadi. Ai ko ke ma za ki iya lura cewa duk wanda aka yi wa irin wannan shaken nan da nan suke fara tari, idan ma ba su fito sun shaki iskar gari ba, nan da nan numfashi zai iya sarkewa.

Tabbas mun san akwai mata wadanda za a ce su rika shiga hayaki domin gyaran jiki. To inda illar take shi ne wai wadansu sai sun rufa da hayakin cikin wani zane ko bargo. To a irin wannan ne akan samu matsala, a ce sai an shiga an lullube, ga hayaki a ciki. Idan ta kama dole, sai dai kawai a ce matar ta saka wani takunkumi a fuska mai tace hayaki ya bar iska kafin ta shiga, kuma na kankanen lokaci, wato ’yan mintoci kadan a leko a shaki iska sa’annan a koma (kamar yadda wadansu masu iyo a ruwa sukan yi), idan kuma ba haka ba nan da nan za ta ji kamar numfashi zai sarke. A wannan zamani ma a yanzu mun san akwai irin wadannan wurare na gyaran jiki na zamani wadanda watakila suke da kayan aiki na zamani irin wadanda ba za su sa mace ta samu wata illa ba.

Ai ko irin hayaki wanda ake sa wa don daki ai ana so ne a sa ba tare kowa na ciki ba. Idan ya gama aka kashe wutar a iya shiga. Duk kuma zance daya ne da sauran hayaki, misali irin na igiyar Leko domin kashe sauro. A saka turaren a kulle dakin kada a bar kowa ya shiga, idan ya turara sai a kashe hayakin a bude tagogi ya sarara kafin a shiga.

 

Yaro ne shekararsa biyu da rabi. Da yana magana lafiya kalau amma a kwanakin nan ya fara in’ina. Ko hakan na da wani dalili? Kuma wane mataki ya kamata mu dauka?

Daga Khalid T. Kaduna

 

Amsa: Eh, dama ai in’ina daga shekara 2 na haihuwa akan fara ta, lokacin da yaro ya fara yin furuci. Yana da kyau ka kai shi asibiti a duba shi a asibiti wanda ke da bangaren koyon furuci wato speech therapy. A kwanakin baya wata mai karatun wannan shafi ta bayyana mana cewa akwai wannan sashe a Asibitin Kunne na Kasa da ke nan Kaduna.