Search
Subscribe
Ko kun san kida na taimaka wa shanu wajen kiwo?

Wani manomi yana saka kixa ko waka ga shanu a Kenya

Ko kun san kida na taimaka wa shanu wajen kiwo?

Manoman garin Meru da ke kasar Kenya sun gano tasirin da kade-kade musamman na rege (reggae) ke yi wajen kwantar da hankalin shanu inda suke samun natsuwa ta hanyar sauraron kade-kaden da hakan ke sanya su samar da madara fiye da yadda za su samar idan ba su saurari kade-kaden ba.

Wannan fasaha, wacce aka gano tana sanya nishadi da natsuwa ga dabbobi tamkar yadda dan Adam ke ji yayin sauraron kade-kade. Masanan sun gano cewa baya ga natsuwa da samar da madara mai yawa, kidan kan kwantar wa dabbobin hankali da samar musu da isasshen barci mai dadi.

Wannan gwajin ya biyo bayan kwana kadan ne da Shugaba Uhuru Kenyatta ya kaddamar da ginin wajen samarwa da kuma sarrafa madarar shanu na kimanin Shilling Kenya miliyan 250 (kimanin Naira biliyan daya) a garin Meru.

Binciken masana ya tabbatar da cewa, sauraron kida na taimaka wa kwakwalwar dan Adam wajen samar da natsuwa da kuma inganta lafiyar jiki daga gajiya. Sun ce ba kawai a nan amfaninsa ya tsaya ba, domin hatta wartsake jini da ba shi damar gudana yadda ya kamata a jikin dan Adam tare kuma da sassauta radadi a jikin mutum.

Shugaban kamfanin samar da abubuwan da ake yi da madara na Meru Highland, Mista Justus Nguu, ya ce manoma da dama na amfani da samfurin kidan reggae wajen natsar da shanunsu da kuma samar da madara mai dimbin yawa.

Nguu, ya bayyana cewa, a yayin da saniya ta kwantar da hankalinta waje daya ta hanyar sauraron kida, hakan kan taimaka mata wajen samun lafiyayyen barci wanda a sakamakon haka, take samar da madara mai yawa.

“Wannan ya tilasta wa manoma da dama koyon sabuwar dabarar, ta hannun kamfaninmu na Meru, kuma sabuwar cibiyar da ake ginawa da za ta rika samar da lita dubu 100 a garin Nyambene za a kammala ta zuwa nan da watan Oktoban bana,” inji shi.

Bincike ya gwada sauraron kida a gab da lokacin da za a yi wa dabbobi tiyata ma na taimaka wa wajen samun nasara.

“Wannan ya biyo bayan tabbacin da gwamnati ta bayar ne a kokarinta na inganta walwalar manoman da suka dogara  kacokan kan samar da madara don ci da iyalinsu,” inji shi.

Shugaban Kenya ya shawarci manoman yankin su yi amfani da wannan damar idan an kammala wajen kara adadin madarar da suke samarwa.

Ba kamar sauran wuraren sarrafa madara na KCC ba, ita wannan cibiya da ake ginawa za ta rika tafasawa tare da inganta madarar kafin a kai sauran wuraren sarrafawar da ke sauran yankuna biyar na kasar da suka hada da Tigania ta Gabas da Tigania ta Yamma da Tigania ta Tsakiya da Igembe ta Arewa da kuma Igembe ta Kudu wadanda a yanzu haka kungiyoyin kananan manoma da sauran kungiyoyin taimakon kai-da- kai ke amfani da su.

 

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin